Sheikh Gumi ya ƙaddamar da ƙungiyar kare haƙƙin Fulani makiyaya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shaharren malamin  addinin Musuluncin nan da ke Kaduna, Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Gumi ya kafa ƙungiyar da za ta kare haƙƙin Fulani makiyaya.

Gumi ya sanar da kafa wannan ƙungiya da ya kira Nomadic Rights Concern, NORIC a taƙaice a yayin gudanar da tafsirin watan Ramadan a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna a arewacin Nijeriya.

Ya ce ƙungiyar za ta janyo hankali al’umma a game da cin zarafin Fulani makiyaya da ake yi.

Ya bayyan Farfesa Umar Labbo a matsayin wanda zai jagoranci ƙungiyar, yana mai cewa NORIC za ta zama wata kafa da makiyaya za su kai ƙorafe-ƙorafensu a game da abubuwan da ke ci musu tuwo a ƙwarya zuwa ga hukumomin da suka dace.

Ya ƙara da cewa makiyayan za su kai ƙorafinsu wajen ƙungiyar NORIC, wadda ita za ta taimaka musu ta wajen ɗaukar mataki na shari’a.

Dr. Ahmad Gumi yana kan gaba-gaba wajen kira ga gwamnati da ta samar wa Fulani yanayi mai kyau don inganta rayuwarsu da ta ‘ya’yan su musamman wajen ba su ilimi da samar musu da ƙoramun kiwo da sauransu.

Gumi ya sha yin kira gagwamnati da zauna da varayin daji masu garkuwa da mutane don jin koken su, wanda ya ce hakan zai samar da sulhu a tsakanin al’umma.