Sheikh Nuru Khalid zai soma limanci a wani sabon masallacin Abuja

Daga BASHIR ISAH

Fitaccen malamin nan na Abuja da ya rasa matsayinsa na limamin masallacin rukunin gidajen ‘yan majalisar tarayya da ke Apo, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya ce an naɗa shi babban limamin sabon masallacin Juma’a da aka buɗe a bayan rukunin gidajen CBN da ke Abuja.

Sheikh Khalid ya bayyana sabon naɗin nasa ne yayin zantawarsa da jaridar Vanguard ranar Litinin a Abuja, yana mai cewa Juma’a mai zuwa, 8 ga Afrilu zai soma jagorancin Sallar Juma’a a sabon Masallacin.

Kwamitin Masallacin Apo ya tsige Sheikh Khalid daga limanci ne saboda huɗubar da ya yi a kan matsalar tsaron da ta addabi Nijeriya.

Sheikh Muhammad Nuru Khalid ya ce an tsige shi ne saboda nuna damuwarsa da ya yi a kan yadda talakawan ƙasar nan ke fama.

Daga nan ya ce, bayan da ya rasa limanci a tsohon masallacinsa, sai wani sabon masallacin Juma’a da ke bayan CBN kwatas ya naɗa shi limanci inda ake sa ran zai soma jagorancin Sallar Juma’a a Juma’a mai zuwa, wato 8 ga Afrilun da ake ciki.

A cewar malamin, “Tsige ni da aka yi manuniya ce game da yadda Nijeriya take a yau. Mutane da daman gaske na fakewa da addini suna aikata abubuwan da ba su dace ba.

“Irin waɗannan mutane za su yi dukkan mai yiwuwa wajen kawar da mutane iri na masu faɗin gaskiya don amfanin talakan Nijeriya. Wannan shi ne irin abin da kan faru da duk wanda ya nuna damuwarsa a kan wahalar da talakawan ƙasa ke sha.