Shekara 52 na mulkin Alafin na Oyo, Lamidi Olayiwola Adeyemi III, sun ƙayatar – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya jajenta wa gwamnatin Jihar Oyo da al’ummar jihar kan rasuwar Sarkin Yarabawa Alafin na Oyo, Lamidi Olayiwola Adeyemi III, ranar Juma’a.

Buhari ya bayyana shekara 52 da sarkin ya shafe a karagar mulki da “masu ƙayatarwa ta hanyoyi da dama” cikin wata sanarwa da kakakin fadar shugaban ƙasa Femi Adesina ya fitar.

A ranar Asabar aka yi jana’izar sarkin a tsohon garin Oyo, inda aka binne shi a farfajiyar masarautarsa.

Masarautar Oyo ta ce ya rasu ne a ranar Juma’a yana da shekara 83 bayan ya yi jinya a Asibitin Koyarwa Jami’ar Afe Babalola a Ado Ekiti, babbar birnin jihar Ekiti da ke Kudu maso yammacin Nijeriya.

Shugaban ya yi addu’ar Allah ya jiƙan sa, yana mai cewa “na tuna irin kalaman hikima da ya dinga yi a duk lokacin da ya halarci tarukan ƙasa”.

Shi ne sarki mafi daɗewa a kan gadon sarautar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *