Daga HASSAN IMRAN
Assalamu Alaikum. ’Yan uwana, yau na zo da wata taƙaitacciyar nasiha ne kan yanda za mu ciyar da ƙasarmu gaba bayan cikar ta shekara sittin da huɗu da samun ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka, nufin ba da shawarwari da samar da mafita.
Masana sun ce a halittar ɗan’adam an sanya masa son abubuwa da yawa na jindaɗi da kuma morewa. Daga cikin abinda aka sanya sonsa a zuciyar ɗan’adam akwai kishi da son ƙasarsa. Kishi da son ƙasa na nufin aikata wasu ayyuka da za su kawo cigaba mai ɗorewa a cikin al’umma. Misalin bin doka da oda, kare kayan gwamnati daga kowace irin ɓarna; ko kuwa lalata su, satarsu ko kuma rushe su. Harwayau, mu sani cewa kula da tarbiyya ‘ya’yanmu na daga cikin abubuwan da za su kawo wa ƙasarmu cigaba. Duk ɗan da aka tarbiyyantar da shi akan tarbiyya tagari, zai zamo abin alfahari da kuma silar da zai haɓaka cigaba a cikin al’umma. Amma duk ɗan da bai samu tarbiyya tagari ba zai zamo barazana ga ƙasarsa da kuma al’ummarsa.
Idan muka dawo kan muhimmancin ƙasarmu, abin sani ne cewa a cikinta aka haife mu kuma a cikinta muka rayu; kuma iskar ta muke sheƙa, kuma abincin cikin ta muke ci. Hakazalika, a cikin ta muke neman ilimi kuma a cikin ta muka nemi sana’ar ko kuwa aikin dogaro da kai.
Daga cikin dalilan dake nuna mana kimar kishi da son ƙasa a zuciyar ɗan’adam sun haɗa da abinda ya faru da Manzon Allah (tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi) yayin da maƙiyansa daga cikin mushrikan ƙuraishawa suka matsa masa har ya kai suka kore shi daga garin Makka. Masana tarihi sun ce lokacin da Manzon Allah ya fita Hijirarsa daga Makka zuwa Madina, a yayin da ya kai wani wuri da ake kira da sunan “Hazwaraa” sai ya juya baya ya fuskanci Makka cikin baƙinciki da takaici, yana mai cewa, “Wallahi ke ce mafi soyuwar ƙasa a gare ni, da ba don mutanen ki sun fitar da ni ba da bazan bar ki ba.”
Bugu da ƙari, a duk lokacin da Manzon Allah (SAWA) ya yi tafiya wajen garin Madina, a yayin dawowarsa da ya hango gine-ginen gidajen Madina sai ya ƙara sauri saboda shauƙin shigarsa garin. Tabbas ne masu iya magana na cewa, “Duk wanda ya bar gida, gida ya bar shi.”
A wannan mako mai ƙarewa, Nigeriya ta cika shekara sittin da huɗu da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka. Amma shin ko kwalliya ta biya kuɗin sabulu?
Shugabanin mu da jagororin mu na baya irin sun Sardaunan Sokoto, Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa, Obafemi Awolowo da sauransu duk sun nuna wa ƙasarmu kishi da so na gaskiya wajen inganta rayuwar al’ummarsu da kuma kawo cigaba a cikin ƙasar. Masana da Shehunan Malamai irinsu Shaikh Abubakar Gumi da kuma Malam Aminu Kano sun bada gudummawarsu wajen ciyar da yankin Arewa gaba. Amma yanzu Arewa tafi kowanne ɓangare a ƙasar nan fuskantar kowacce irin matsala da kuma rashin cigaba. Dole ne mu wa kanmu karantun ta natsu mu waiwayi baya, domin maganta matsalolin mu.
Hanyoyin da za mu samarwa wannan ƙasar tamu cigaba na da yawa, daga ciki akwai yawaita yin addu’a domin Ubangiji ya shige mana gaba cikin ƙalubalen da ƙasarmu take fuskanta, domin babu abinda ya fi ƙarfin addu’a. Haka kuwa da shugabanni da mabiya, kowa na da gudunmawar da in ya aikata zai kawo cigaba a ƙasar nan. Gudunmawar shugabanni shi ne tabbatar da adalci a dukkan harkokin gwamnati da kuma samar wa al’umma sauƙi a harkokin rayuwa da kuma samar masu abubuwa more rayuwa. Sa’annan kare masu rayuka da dukiyyoyinsu, sauƙaƙa masu hanyoyin samunsu da kasuwanci, samo masu ruwa da wutar lantarki da sauran su.
Gudunmawar mabiya ya ƙunshi yin biyayya ga shugabanni da kuma taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri da za su taimaka masu sosai wajen kawo ƙarshen kowannee irin nau’i na ta’ddanci. Sa’annan kula da kayan gwamnati wanda an yi su ne domin amfanin jama’a gaba ɗaya. Abin takaici da ban haushi ne yadda wasu matasa a cikin mu suke lalatawa, satar su ko kuma rushe wasu kadarorin gwamnati, musamman a duk lokacin da wani rikici ya ɓarke ko kuma wata zanga-zanga ta taso.
Allah Ya shige wa shugabannin mu gaba Ya kuma datar da mu a dukkan harkokinmu na yau da kullum. Allah Ya kawo mana dawamamme cigaba a ƙasarmu Nijeriya. Amin.
Hassan Imran ya aiko da wannan nasiha ne daga Jos, kuma za a iya samun sa kan addreshinsa ta imel [email protected]