Shekaru ma fi hatsari a tarbiyyar ’ya mace

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Yau za mu yi magana a kan shekarun da dukkan mace baliga take jin kanta, daga shekara goma sha huɗu zuwa Shekara Ashirin. A lokacin ne da maƙerin halitta na ‘yanmatantaka ya nuna a jikin mace. Wato komai nata ya fito na budurci, ta ƙosa kenan. To lokacin ne uwa kuma za ta shiga yanayi na damuwa da rayuwar hatsari ga yaranta mata da suka shiga wannan shekarun sai ta ɗauki kyakkyawan  mataki, da sa ido sosai a kan yaranta mata.

Wannan su ne shekarun da iyaye ke cewa ma fi hatsari a kan iyalinsu don lokacin ne fitina kala-kala za ta fara bayyana. Da zarar uwa ta ga wannan lokacin ya yi, to ta fara jan yaranta mata a jiki tana koya musu abubuwan da za su kiyaye da yadda za su yi shiga da mu’amalar da za su yi da maza ko da kuwa maharramansu ne.
Lokacin ne da su kansu suna jin kansu sun girma, abubuwan sha’awa na motsa musu. Sai uwa ta yi nazari ta yadda za ta fuskantar da su irin hatsarinsa a rayuwarsu. Amma idan uwa ta yi sakalele da rayuwarsu ta bar su suka gane wasu abubuwa marasa kyau, kuma suka yi nisa a ciki, to ta yi kuka da kanta ba yaranta ba. Wasu iyayen kunya ke hana su nusar da yaransu cewa, da da, da yanzu ba ɗaya ba ne. Lokacin da suke shekara bakwai ko goma daban, a kan yarinya ta haura goma sha. To dole sai an mata huɗuba ko Duniya ta yi mata.

Idan dai ba haka ki ke so a yi ba, uwa ta gaya wa ɗiyarta gaskiya ta gaya mata: “yanzu kin  girma kin fita sahun wasa mara kan gado, ki guji nuna tsiraici a gaban kowa ko da kuwa maharramanki ne”. A nuna mata yadda za ta sa kaya na mutunci, ta tsare mutuncinta, A hana ta wasa barkatai ko da kuwa da ‘yanuwanta mata ne. A nuna mata iya ita kanta kaɗai za ta yarda da kanta. Yanzu ta wuce duk wasu abubuwa marasa kyau. Uwa ta koya wa ɗiyarta yadda za ta sa kaya na mutunci ba wanda za su fito mata da tsiraici ba, da sunan gayu. Sannan uwa ta sa wa ɗiyarta ido duk inda za ta, a ba ta lokaci. Sannan idan kin fita duk namijin da ya kira ki, kar ki je. Idan da gaske yake, ya zo gidanku ya yi magana da iyayenki, su za su san wanne iri ne shi. ya kamata ku yi mu’amala da shi ko a’a? Kada ki yarda namiji ya ja ki wani guri da sunan zuwa hira ko hutawa. Daga nan sha’ani ya ɓaci, muddin za ki bar yarinya sakakkai ko ina tana zuwa ba tare da kin sani ba, to kin saya mata tikiti lalacewa da kanki.

Yawan ganin sababbin ƙawaye tare da ɗiyarki wannan ma abun dubawa ne. Yana da kyau ku binciki daga inda ta samo su, ina ma suke zuwa, kuma me suke yi. Muddin ba za ki tsawatar ba, su ne Ummul-aba’isin lalacewarta.

Yawan kyauta ko kayan da ba ki saba gani ba ki gani a hannunta, yana da kyau ki san a ina take samowa, kuma waye yake ba ta. Idan ba haka ba, magana ta gama lalacewa, shi dai itace tun yana ɗanyensa ake tanƙwara shi. Don haka aiki ne babba ga iyaye su tallafa wa yaransu matasa yadda za su yi rayuwa, ba su sa musu ido ba.

Wasu iyayen har murna suke wai ‘yar su ta yi farin jinin samari. Wannan ya zo, wancan yazo, wani ya ba ta waya, wani ya ba ta kayan ado. Kin washe baki har faɗa kike cikin jama’a ke ‘yarki Allah ya kashe ya ba ta, ba ta da matsala. Wayyo! Aiki babba ne wannan kuma babbar matsala ki ka ɗibo mata. Domin maza dai ba sa ba da kyauta a banza sai dai inda suka san za su amfana daga ɗiyarki. Muddin ba ki kula ba, to kwaɓarki za ta yi ruwa tsululu ma kuwa.

Iyaye maza sai sun kula da yanayin rayuwar yaransu kar su ce za su bar wa uwa ita ɗaya ta yi wa ɗiyarsu tarbiyya. Ya kasance kana ba da gudunmawa kai ma kar a yi wa ɗiyarka ido mara kwalli. Amma idan ka biye wa mace da surutunta na wai ka takura wa yarinya, to wallahi za ku yi da-na-sani mara daɗi. Gara ka haɗa gabaɗaya ka yi musu fata-fata in dai ka san matarka ba ta da zafi, to ka yi mata dole a kan tarbiyyar ɗiyarka kafin ta rusa maka gida.

Yawancin iyaye sakaci da rashin ɗaukar mataki, ko nunawa uwa da ‘yarta soyayya ke hankaɗa mace tai ta cin karenta babu babbaka.

A wannan lokacin ne uba yakamata ya kula da buƙatun yarsa; kamar audugar mata duk wata, a yi ƙoƙari a sama mata. Don wannan na ɗaya daga abin da ya dace a gurin ɗiya mace tana buƙata idan ba ka ba ta ba, ina za ta je ta  samo? Ka ga da kanka ka tura ta ta nema ko ta wacce hanya. Yanzu lokacin saka ƙunzugu ya wuce, da ne ake yi. Yanzu abu ya zo da zamani, sai dai audugar dole. Don Allah a rufe ido a ba ta sai a zauna lafiya.

Mai na shafawa, kayan kwalliya, duk waɗannan suna cikin tsarabar mata da suke buƙata. A yi ƙoƙari a ba ta gudun faɗawa rayuwa mara daɗi. kada a bar yarinya ta koyi ciye-ciye marasa kan gado, ranar da baka da shi ko uwar ba ta da shi, wa zai ba ta? Dole fa sai an tsara wa yara rayuwa da yadda ta ke tafiya. Muddin aka sa musu ido, akwai babbar barazana wallahi.

Masifar da ta kunno mana yanzu ita ce waya. Wannan aba tana rushe mana tarbiyyar da muka ba wa yaranmu. Za ka ga yarinya kamar ta gaske ko hannu ka sa mata a baki ka ce ta ciza, ba za ta ciza ba. Amma wallahi waya ta sa ta cikin muguwar rayuwa da ba ki/ba ka taɓa zata ta faɗa ba. Don haka, iyaye mu rage sangarta yara da ba su waya. Wayar nan ba ƙaramar illa take wa yaranmu ba. Ba ga matan ba, ba ga mazan ba.

Kada a yarda saurayi ya ba wa yarinya waya. Idan iyaye sun gani, su karɓe don ba abin arziki suke shukawa ba, wallahi. Amma muddin kuka bar yara su yi yadda suke so, to kun sakar wa samari ragamar juya rayuwar yaranku, kuma daga baya za ku yi kukan da ba shi da amfani. Maganin abu, kar a fara. Don Allah iyaye mu kira yaranmu mu sanya su a jikin, mu zama masu nuna musu rayuwa. Mu tsoratar da su illar fitina da kuruciya. Gaba ake ji da ba ta da baya. Lokacin da za su yi nadama idan ya zo, to ku iyaye da ku za su yi kuka. Ku za su tsana, su ce ma  ku ne kuka jawo musu, saboda ba ku ba su rayuwa ta gari ba.

Amma idan tun farko kin gaya mata illar abun, to dole za ta kiyaye, ta tsani abun, ta ƙyamaci mu’amala da mutanen da ta san ba su da tarbiyya har ma ta koya musu su zubar da abunda ba shi da kyau. Kin ga an samu cigaban da har ta taimaki wasu ma. Sai su tashi da kyakkyawar tarbiyyar da kowa zai yi sha’awa.

Amma iyayen dake gudun yaransu da sunan wai kunyar ‘yar fari abun ba kyan gani. Ta yaya za ki wofantar da ‘yarki ga duniya, ba ruwanki da ita, komai za ta yi sai ki yi shiru, ki bar ta da sunan ‘yar fari? Sai ta lalace, ki zo kina kuka, yar farin wa? Ki nutsu ki ja ‘yarki a jiki, ki ba ta tarbiyya ta gari, ya fi ki ajiye ta ba mai gaya mata, kuma ba ruwan Allah. Wallahi sai ya yi muku hisabi a kan amanar da ya ba ku.

Allah ya sa mu dace, mu fi ƙarfin zuciyarmu, mu yi aiki da abunda ya ke na daidai. Mu haɗu sati na gaba, cikin yardar mai dukka. Ma’asallam.