Shekaru shida na kwashe Ina ƙirƙirar baƙaƙe da lambobin Hausa – Sadar Musa

“Hausa harshe ne dake da rinjayen masu amfani da shi a Afrika”

Daga AISHA ASAS a Abuja

Idan ana zancen baiwa ta rubutu, ba na jin a faɗin Nijeriya akwai inda ya kai Arewa yawaitar marubuta da za a iya bugar ƙirji a kira su da gwanaye. Wataƙila namijin ƙoƙarin da suke yi ne ya haifar da wanzuwa da kuma raya yaren Hausa ga masu tasowa duk da irin horo da ruɗin da yaren Ingilishi ke yi a ƙwaƙwalensu. Cikin irin wannan ƙoƙari, aka samu wani matashi da ya yi kishin ƙirƙirar baƙaƙe da kuma lambobi da malam bahaushe zai buge ƙirji ya kira nashi ba wanda ya aro daga Larabci ko Ingilishi ba. Ku biyo mu a tattaunawar, don jin mafari da tushen wannan namijin aiki da matashin ke yi. Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Sadar Musa: 

MANHAJA: Ka fara da gabatar da kanka ga masu karatu.

SADAR: Sunana Sadar Musa. Daan asalin garin Kano, An haife ni a unguwar Kurna Naira da Kobo,  Dala L.G,  a watan January,  shekarar 1991. Na yi karatun primary a Gobirawa Special Primary School, bayan na kammala,  na tafi Junior Secondary School, Gogau, daga nan na tafi Government Technical School,  Kwakwaci, inda ban kammala ba sai na tafi makarantar Government Senior Secondary School, ƙofar Nasarawa,  anan na kammala karatuna na secondary, bayan nan na tafi makarantar gaba da secondary, Kano State Polytechnic na yi ‘National Diploma’ ɓangaren ‘Marketing’, bayan na kammala yanzu na ɗora Ina digiri na na ɗaya a “National Open University” akan Harshen Hausa. Kuma Ina taɓa kasuwanci daidai gwargwado.

Shin za a iya kiran ka da marubuci?

Eh toh! zan iya ce miki eh! duba da a baya na shiga harkar rubuce-rubuce, amma kuma na bari, saboda wasu dalilai, zan iya cewa,  abin da nazo da shi ya banbanta da rubutu duk da alƙalami ne ya bada gudunmawar samuwar su waɗannan baƙaƙe, ma’ana ansamar da ƙirƙira aciki, ko na ce na ƙirƙiri sababbin baƙaƙen Hausa waɗanda na samar da su ta hanyar da a da babu su,  kuma hakan ya bada damar da za a iya rubutu da su,  kuma a karanta abun da aka rubuta, har yakai matakin da ayanzu Ina koyar da darasi na musamman ga ɗalibai a duk ƙarshen mako.

Yanzu haka Ina rubuta litattafai da dama domin samun ingantaccen ilimin shi wannan sabon rubutu na harshen Hausa, a don haka bazan guji a kira ni marubuci ba da kuma wani suna da ya dace da abin da nake yi.

Kwanakin baya mun samu labarin wani aiki da ka ke yi don kawo sauyi a rubutun Hausa. Shin za ka iya sanar da mu wannan aikin da kuma dalilin yin tunanin samar da shi?

Ƙwarai da gaske haka ne maganar ki, amma ba sauyi zan kawo ba,  cigaba zan kawo ko na kawo wa rubutun Hausa dama kuma shi yaren, dalili kuwa shine,  a yanzu haka muna amfani da rubutun Ajami da na Hausar boko, kuma dukkannin su ba na mu ba ne,  na aro ne, wancan ajami na Larabci shi kuma na boko na Birtaniya (English), tun da Allah ya bani damar ƙirƙirar waɗannan baƙaƙe da za ayi amfani da su a rubutun Hausa to, kinga za mu ce harshen Hausa ya samu cigaba ba sauyi ba.

A tunani na sauyi kamar dama can harshen yana da rubutun sa ne,  nakan sa kuma ya samu sauye-sauye to kuma dama can harshen na mu bai da nashi rubutu nakan sa sai na aro da muke amfani da shi.

na yi ƙoƙarin samar da sababbin baƙaƙen Hausa wanɗanda ba mu da namu sai na aro da muke amfani da su, baƙaƙe ne manyan baƙi da kuma ƙananun baƙi,  adadin su guda 37,  sa’annan na samar lambobi daga sifili zuwa tara, kin ji yadda tsarinsu yake.

Na fara tunanin samar da waɗannan baƙaƙen dalilin kishin harshenmu na Hausa da kuma son cigaban yaren a duniya, harshen Hausa babban harshe ne da yake da rinjayen masu amfani da shi a harsunan Nijeriya da Afrika dama duniya gabaɗaya, ganin haka na fara tunanin ya kamar wannan harshe da Allah ya yi wa baiwa da girma da kuma daraja a duniya,  amma ba shi da rubutunsa nakan sa,  duba da akwai ƙananun harsuna waɗanda ba su kai harshen Hausa ba,  amma za kiga suna da nasu rubutu ko da kuwa suna amfani da wani rubutun da ba na suba, wannan shi yake ba wa waxannan harsuna damar ƙirƙire-ƙirƙire, ƙere-ƙere da ma fito da duk wata fasaha da za ta kawo musu cigaba da wuri, na yi tunanin toh ya za’ayi mu ma namu harshen ya samu nasa rubutu nakansa koda za mu yi amfani da na aro, wannan ya sa na yi ƙoƙarin fara wannan aikin shekara goma da ta gabata, kuma na ɗauki kimanin shekara shida Ina aikin, yanzu haka da kammala aikin na yi shekara biyu muna tuntuvar waɗanda ya dace don tabbatuwar amfani da wannan rubutu a makarantu.

Zuwa yanzu ana kan wacce gaɓa a wannan aikin na samar da sababbin baƙaƙen na Hausa?

A yanzu za mu ce, alhamdu lillah,  haƙar mu ya kusa cimma ruwa,  saboda shekara biyu kenan da kammala aikin na samar da waɗannan baƙaƙe, da yake kafin na kammala aikin Ina yi ne ni kaɗai ba tare da tuntuɓar nagaba ba,  sai bayan da na kammala a waɗancan shekarun na fara tuntuvar masana domin neman shawara, gyara da kuma ƙarin haske akan waɗannan baƙaƙe, musamman manyan maluman mu na ɓangaren sashen koyar harsuna, wasu daga cikin ‘professors’ ɗin mu da ma wasu daga cikin maluman mu na makarantu daban-daban domin mu girmama su kuma mu nemi shawarar su,  kuma alhamdu lillah duk suna ba mu goyon baya yadda ya da ce, dan haka zan iya cewa muna gaɓar da an kusa kammala komai don fara gabatar da ilimin wannan rubutu a makarantun mu In sha Allah. 

Kuma mun yi nisa wajen koyar da wannan rubutu a ‘lesson’ da muke yi kamar yadda na faɗa abaya, nan ba da daɗewa ba za mu buɗe ‘private lesson’ a sassa daban-daban domin masu ra’ayin koyon ilimin tunda mun samu damar yin haka a hukumance. 

Nan gaba kaɗan za mu fara gabatar da koyar da darrusa a tashar mu ta YouTube da yardar Allah,  yadda al’umma za su sa mu damar shiga su koyi wannan rubutu da yadda ake karanta shi, hakan zai zama abu me sauqi ga waɗanda ma’aikata ne ko kuma suna nesa ko waɗanda ‘yan kasuwa ne ba su da lokacin zuwa aji.

Ko me ya sa ka ke ganin rubutun Hausa na buƙatar wannan canjin?

Saboda bunƙasar harshen a duniya da kuma masu amfani da harshen, akwanan nan masana sunyi bincike Hausawa masu amfani da harshen Hausa sun kai kimanin mutane miliyan cassa’in (90), ban da waɗanda koyon yaren suka yi,  suka iya shi, akwai ƙasashe banda Nijeriya da harshen Hausa shi ke da rinjaye wajan amfani da shi a waɗannan ƙasashe, ko kuma wani kaso mai tsoka musamman ƙasashen Afrika, kamar Nijar, Kamaru, Chadi, Kwatano, Togo, Ghana, Kwadebuwa, Mali da sauran ƙasashe da yawa na Afrika da sassan duniya, toh kinga iya haka ma harshen ya yi bunƙasar da yakamata ace yana da nashi rubutun, hakan zai ƙara daraja da qima ga harshen, zai kuma zamo alfahari awajen mu mu Hausawa aduk inda muka tsinci kanmu, musamman ɓangaren ilimi.

Muna da masu fasaha ta ɓangaren rubutu da ƙere-ƙere a Nijeriya dan haka koyar da wannan ilimi a makarantu zai bada damar matasan mu su fi gane abubuwa da dama ta fuskar koyarwa a makarantu da shi wannan salon rubutu.

Kasancewar an jima bisa wannan tsari na rubutun Hausa, ba ka ganin hakan zai iya kawo tasgaro ga burin naka na ganin an koma amfani da waɗannan sababbin harufa?

Kinyi tambaya mai mahimmanci anan, kuma tabbas an shafe kimanin shekara sama da ɗari biyu 200 ana amfani da rubutun aro na Birtaniya,  amma hakan bazai zama hujja ga duk wani bahaushe cewa nashi rubutun bazai karɓu ba ko kuma bazai je inda sauran rubutu na duniya suka je ba, wannan bazai zama dalili ba sakamakon kowane abu na duniya yana fara wa daga ƙarami ya zama babba ko menene, ganin hakan nake son ba wa ‘yan’uwa na hausawa dake faɗin duniya shawarar mu karɓi wannan al’amari, mu koya, mu yaɗa shi domin namu ne, mu yi amfani da shi ta hanyar ilimi da saƙonni, domin samuwar wannan rubutu burin mu ne ba iya buri na ba ni da na samar, muna da manufofi masu kyau game da wannan rubutu daga cikin manufar na samar da waɗannan baƙaƙe akwai sama wa harshen Hausa hanyar rubutu na uku kamar yadda ake amfani da rubutun ajami da kuma na Hausar boko.

To,  idan kin lura ba ya daga cikin manufar mu samar da waɗannan baƙaƙe dan a daina amfani da waɗannan rubutu musamman na Ajami da kuma Hausar boko, zai zama harshen Hausa yana da hanyar rubutu na uku kenan wannan shi zai ba wa gwani a ajami damar koyan wannan sabon rubutun da gwani a fannin rubutun boko damar koyan wannan rubutu, kuma Ina ganin idan al’umma suka karɓi wannan rubutu hannu biyu,  zai zama duk inda harshen Hausa ya shiga shima zai shiga, kuma al’ummar Hausa su saka aransu ba na wani ba ne na su ne, hakan zai taimaka wajen duk inda ilimin ya shiga zai 1yi tasiri, saboda rubutu ne da yake da sauƙin koyo kuma wanda ya koya zai iya da wuri, yanzu kinga Ina da ɗalibai daban-baban kama daga maza da mata manya da yara Ina da ɗalibai yara ‘yan shekara 8 zuwa 10 waɗanda akansu na tabbatar da tasirin sauƙin koyan rubutun da ma karanta shi, adan haka In sha Allah bana fatan za mu samu tasgaro kamar yadda ki ka faɗi.

Kowanne abu yana da tsari da kuma matakalai da ake bi don ganin an kai ga nasara, musamman ma harkar irin wannan ta ilimi. Shin waɗanne matakai ne aka taka don ganin wannan aiki ya kai ga nasara?

Gaskiya ne shi ya sa tashin farko dana kammala wannan aikin na yi ƙoƙarin kauce wa ‘media’ ko yanar gizo, saboda a wannan lokacin bani da tabbacin me mutane za su faɗa akai, sai na fara haɗa kwamiti na mutane guda bakwai, waɗanda zan yi aiki da su ta vangaren samun nasarar wannan aikin kuma a kwamitin aka naɗa shugabanci da sauran matakan da ya kamata wanda har yanzu kwamitin shekarar sa biyu kenan yana nan yana aiki, bayan kafa kwamitin da ni da su sai muka maida hankali wajen gudanar da tafiyar bisa tsari wanda duk abin da za a yi mai muhimmanci sai an tattauna akan shi, haka muka ci gaba da tafiya muna tuntuvar maluman mu masana musamman waɗanda suke vangaren, kuma alhamdu lillah a wannan tuntuvar da muke yi mun samu nasarori da dama ta samun shawarwari masu kyau don ƙara inganta al’amarin da kuma samun goyon baya da qwarin gwiwa akan ka da na sare da abin da nake yi duk rintsi na daure na ci gaba, haka muke ta tafiya har kawo yanzu.

Sannan mun taka matakai da dama na ganin nasara a wannan al’amari na wannan sabon rubutu abinki da harka ta ilimi wajibi ne sai an zurfaffan bincike duk inda ka shiga ka ke son a ba ka goyon baya akai, domin ganin tabbatuwar kyawun aikin, banda xai-ɗaikun malamai da muke ziyarta, mun ziyarci jami’oi da hukumomi na ilimi domin gyara ko shawara kuma alhamdu lillah ana samun cikakken goyon baya da shawarwari wanda babbar nasara da muka samu ita ce, lokacin da na rubuta wa hukumar ilimi ta Kano wasiƙa game da abin da nake yi da kuma abin da nake gani za a yi, ban yi aune ba, ba wayan wasu lokuta sai na ji kira daga wata hukuma da ke ƙarƙashin ta ilimi da ake kira da KERD, bayan na je suka min tambayoyi akan wannan al’amari.

To  daga nan al’amarin ya ɗora mukai tabin matakai tare da su don ganin an yi abin cikin inganci a hukumance, muna aiki tare da su sai suka turawa jami’ar Bayero da wasiƙa tare da ‘document’ na baƙaƙen da lambobi, domin su yi nazari akai kuma su ba wa gwamnati shawara akai, bayan wani lokaci jami’a ta dawo wa da gwamnati amsar wasiƙar da ta tura mata cike da karɓuwa da kuma gwala-gwalan kalmomi da kuma shawarwari guda uku zuwa huɗu, suka nuna min hanyar da zan bi dan na ƙara ingancin ilimin rubutun, ya zamo yabzauna da ƙafarsa kamar yadda kowanne ilimin rubutu yake a duniya.

Wannan ba ƙaramin farin ciki ya saka ni ba, ganin yadda har jami’a ta yi na’am da wannan al’amari har kuma ta bani shawarwari don ganin an ƙara inganta ilimin, wanda kowa ya sani jami’a ba ta yin abu da ka, sai ta yi bincike sosai kafin ta yarda da kowane al’amari musamman vangaren ilimi sabo irin wannan. Gaskiya na ji daɗi, na yi alfahari da hakan, domin wannan ba ƙaramar nasara ba ce ga al’ummar Hausa, sai dai mu ƙara gode wa Allah (S.W.A) wanda har yanzu muna nan muna aiki da hukumar ilimi da kuma jami’a don yanzu haka akwai littattafai da nake rubutawa wanda jami’a ta bani shawarar na samar da su da zarar na yi gyaran da ta bani shawara akai kuma littattafan sun ƙunshin yadda ake koyan ilimin rubutun a sauƙaƙe da kuma litattafai na ɗalibai, wanda da zarar na kammala su in sha Allah muke sa rai za a nazarce su, sannan a fara koyar da ilimin a makarantun gwamnati, wannan ma ba ƙaramar nasara ba ce da al’ummar Hausa ta samu.

Ta wacce hanya ka ke ganin za su iya samun karvuwa ga mutane?

Ta hanyoyi da dama, misali akwai Hlhanyoyin sadarwa na zamani da muke da su yanzu wanda waɗannan hanyoyin suna daga mafi sauƙin isar da saƙo zuwa ga al’umma, daga ciki akwai wannan hanyar da muke magana da ke ta jarida, ita ma hanya ce me sauqi da wasu waɗanda muke shiryawa don ganin an samu sauƙi wajen fahimtar da mutane har su karɓe su, kwananan akwai tashar mu ta YouTube da muka buxe me suna “MuryarHausaAcademy” wannan tasha za ta bada gudunmmawa wajen nusar da al’umma aikin da muke yi a haka za mu bi matakai da har al’umma za su samu ilimin rubutun idan mutum ya maida hankali shima sai ya ƙware har ya koyar da wasu nan gaba.

Za mu nemi ko muna neman haɗaka da ƙungiyoyin marubuta, da na yanar gizo da kuma gidan jaridu irin naku da na talabijin da kuma radiyo da sanar da al’umma mahimmanci wannan rubutu dama yadda ake koyar da shi. Wannan kaɗan kenan daga yadda za mu bi ko muke bi don karɓuwar wannan rubutu ga al’ummar Hausa.

Za mu so jin ko an fuskanci ƙalubale a tafiyar?

Sosai kuwa, duk wani abu me kyau dama sai an fuskanci ƙalubale don haka wani abun ba ya bani mamaki idan yazo min musamman ma nasan wannan wani abu ne sabo da na zo da shi wanda mutane ba su tsammace shi ba, wasu kuma ba su tava tunanin samuwar sa ba, shi ya sa ma idan naje wa wasu da wannan batu sai jikin su ya mutu kuma su kashe min gwiwa da samin tunanin na zo da wani abu me wahala wanda bazai tava yiwuwa ba, din haka na sake tunani, wasu kuma su gayamin zai yiwu, amma zan sha wahala.

Wasu kuma sukan faɗa min gaka matashi baka san wasu ba Ina ma ace kai wani babba ne da ka kai matakin ‘professor’ da shi kenan kakar ka ta yanke saƙa, da irin waɗannan maganganu dai da dama wanda dukkannin su ban kalle su ba ballantana su yi tasiri akaina, abin da nake sawa arai komai ki ka ga ya tabbata to Allah ya yarda da wannan abun shi ya sa zai tabbata, sannan kuma wannan aikin ba na sakawa arai na cewa, nawa ne ni kaɗai Ina haƙiƙance cewa, na al’umma ne musamman al’ummar Hausa, Ina faɗa wa al’umma cewa, ni iya aikina samar da wannan aiki sai kuma koyar da shi ga al’umma har mu samu ƙwararrun malamai a fannin, wanda hakan zai sa cikin ƙanƙanin lokaci mu samu zaƙaƙuran hausawa da za su iya wannan rubutu da karatu wanda hakan zai ba wa al’ummar damar yin amfani da wannan rubutun ta fanni daban-daban musamman harkar rubuce-rubuce da kuma ba da ilimi musamman idan Allah ya karɓi al’amarin, al’umma kuma suka maida hankali wajen ganin tabbatuwar sun yaɗa wannan rubutu aduniya ta hanyar yaɗawa. 

Wani qalubale da na fuskanta ko nake fuskanta akwai matsala da nake samu wajen koyar wa wasu za su ce, wannan ai wahala ne idan na koya me zai amfanar min kuma menene ribata, wasu kuma su ce ai banda abun yi shi ya sa, wasu kuma suna ɗauka ta kamar ban san abin da nake yi ba, sai dai ahankali na fara shawo kan mutane har suka fara shiga aji wanda yanzu haka Ina da ɗalibai da dama, kuma Ina musu uzuri saboda nasan na zo wa al’umma da wani sabon abu da ba su san shi ba; don haka sai na sa wa kaina haƙuri da karɓar kowacce jarrabawar da zan fuskanta daga al’umma don akwai waɗanda na taɓa gayyata kawai suka ƙyalƙyale min da dariya, amma hakan bai sa na janye daga abin da nake yi ba.

Sai kuma ƙalubale ɓangaren kuɗi da yake aiki ne babba ba ƙarami ba, yana buƙatar kuɗi masu yawa wajen gudanar da shi da kuma tabbatuwar sa, amma Ina iya nawa ƙoƙarin wajen yin duk abin da ya dace wajen kashe kuɗi idan buƙatar hakan ta taso, da yake ni ɗan kasuwa ne, Ina amfani ne da abun da nake samu a harkar kasuwa idan wani abu ya taso, amma duk da haka muna buqatar wadatattun kuɗaɗe domin ganin tabbatuwar al’amarin.

Zuwa yanzu ko kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu a wannan aiki?

Eh, alhamdu lillahi. Mun fara samun biyan buƙata musamman ganin yadda al’umma suke ba mu goyon baya, kuma suke ƙaunar abinn tare da buƙatar waɗannan sababbin baƙaƙe, kuma a yanzu shirye-shirye sun yi nisa wajen samar da ‘pont mechanization’ na su waɗannan baƙaƙe wanda a yanzu haka su ne muka fi sa wa a gaba don ganin mun samar da su don amfanin al’umma da kuma ɗalibai.

Domin wannan ita ce hanya ɗaya da za mu samu damar amfani da waɗannan baƙaƙe ta hanyar rubutu da su a kwamfuta kuma mu saka su a manhajar kafafe daban-daban, domin amfani da rubutun, duniya ta zama komai sai ka tafi da zamani musamman a harkar ilimi, shi ya sa muka yi ƙoƙari ganin mun fara shirya darasi a kafafen sada zumunta kamar YouTube da sauran su, kuma muna fatan al’umma za su ba da haɗin kai wajen bibiyar abun da akeyi domin su zama ƙwararru su ma ta wannan fannin musamman idan har suka yarda za su iya.

Mun gode. 

Ni ma na gode ƙwarai.