Sheriff na PDP ya doke Omo-Agege na APC a zaɓen gwamnan Delta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar INEC ta bayyana Sheriff Oborevwori na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Delta.

Wannan ya kasance bisa ga sakamakon da aka sanar a ranar Litinin, Maris 20, 2023, ta Monday Udoh-Tom, Kwamishinan Zaɓen jihar.

Udoh-Tom ya ce, Oborevwori ya lashe ƙananan hukumomi 21 cikin 25 da aka haɗa a jihar inda ya kayar da abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Ovie Omo-Agege.

Oborevwori ya samu ƙuri’u 360,234, Omo-Agege ya samu ƙuri’u 240,229, yayin da ɗan takarar jam’iyyar APGA, Chief Great Ogboru ya samu ƙuri’u 11,029.

A cikin ƙananan hukumomi 25 da ke jihar, Oborevwori na PDP ya samu nasara a 21 daga cikinsu, Omo-Agege na APC ya lashe sauran ƙananan hukumomi huɗu.