Shettima, Atiku da Zulum sun je ta’aziyar rasuwar mahaifiyar Gwamna Dikko Raɗɗa a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya yi ta’aziyar rasuwar Safara’u mahaifiyar Gwamnan Dikko Raɗɗa da ta rasu kwanaki uku da suka wuce a Katsina.

A jawabinsa, shettima ya shaidawa gwamnan cewa ya zo ne a madadin shugaban ƙasa domin miƙa saƙon ta’aziya ga Gwamna Dikko Raɗɗa da al’ummar Jihar Katsina bisa rasuwar mahaifiyar shi.

Ya bayyana rasuwar ta a matsayin babban rashi ga al’ummar Jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya.

Mataimakin shugaban ƙasan yayi addu’ar Allah ya jiƙan ta da rahama, ya sa ta huta.

Haka tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar da mataimakin Gwamnan Jihar Borno Usman Kadafur wanda ya wakilci gwamnan Borno sun kawo ziyarar ta’aziya ga Gwamna Dikko Raɗɗa.

Akwai tsofaffin gwamnoni da ministocin tare da yan majalisar ƙasa, manyan ‘yan kasuwa da sauran al’ummar gari na ta turuwa zuwa gidan gwamnatin Katsina domin gudanar da ta’aziya.

Gwamnonin Kano da Jigawa na daga cikin mutanen da suka halarci jana’izar mahaifiyar gwamnan a garin Raɗɗa cikin ƙaramar hukumar Charanchi a Jihar Katsina.

Ƙungiyoyi irin su ƙungiyar ‘yan jaridu reshen Jihar Katsina da ƙungiyar haɗin kan Funtua da sauran su, sun miƙa ta’aziyar su ga gwamna Dikko Raɗɗa da al’ummar Jihar Katsina.

Ta rasu tana da shekara 93 tabar ya’ya da dama a cikin su akwai gwamnan Jihar Katsina da Hauwa Umar Raɗɗa tsohuwar matar marigayi Umaru Musa Yar’adua.

Ta rasu a wani asibiti a Abuja bayan ta sha fama da rashin lafiya.