Daga BELLO A. BABAJI
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ƙaddamar da majalisar kula da ambaliya da zaizayar ƙasa da fari da gandun daji (NFEDDMC).
Majalisar za ta tabbatar da samar da tsari na warware matsalolin da ke tattare da sauyin yanayi da wasu nau’ukan annoba tare da aiki da hukumomin gwamnati da shiyyoyi.
A lokacin da ya ke magana yayin ƙaddamarwar a Fadar shugaban ƙasa, Shettima ya ce akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa kan ƙalubalen da al’umma ke fuskanta na tasirin iftila’i da ke faruwa akai-akai a Nijeriya.
Samar da majalisar ya biyo bayan shawarwari da aka samu a ƙarƙashin hukumar kula da harkokin annoba daga wani kwamiti da Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ahmed Ododo ke jagoranta bisa umarnin Majalisar Tattalin Arziƙi (NEC).
Shettima ya kuma yaba wa hukumomin musamman kan hasashen yanayin da suka yi a shekarar nan, ya na mai kira a gare su da su yi amfani da damar samun kayayyakin aiki na zamani wajen ayyukansu don samar yanayi mai kyau ga al’umma.
Wasu daga cikin nauyin majalisar sun haɗa da; bai wa gwamnati shawara kan tsare-tsaren kula da annoba, inganta salon kare aukuwar annoba na tsakatsaki da dogon zango da kuma wayar da kan al’umma game da sauyin yanayi.
Ya ƙara da cewa, wajibi ne akan kowacce hukuma ta kasance cikin shiri a kodayaushe sakamakon buƙatar gaggawa a ɓangaren.
Shettima shi ne shugaban majalisar tare da gwamnonin Jihohin Kogi, Bayelsa, Oyo, Ebonyi, Bauchi da Jigawa a matsayin mambobi.