Daga USMAN KAROFI
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya caccaki sabon shugabar jam’iyyar Conservative ta Birtaniya, Kemi Badenoch, kan kalamanta masu zafi ga Nijeriya. Shettima ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin taron tattaunawa na shekara-shekara karo na 10 kan batutuwan hijira, wanda aka gudanar a fadar shugaban ƙasa, Abuja.
A cikin jawabinsa, mataimakin shugaban ƙasa ya ce, “Kemi Badenoch, shugabar jam’iyyar Labour ko Conservative ta Birtaniya, muna alfahari da ita duk da ƙoƙarinta na yin watsi da ƙasar da ta fito. Tana da ‘yancin faɗin ra’ayinta, har ma da cire sunan Kemi daga sunanta, amma hakan ba zai sauya gaskiyar cewa Nijeriya ita ce babbar ƙasa mafi girma ga baƙar fata ba.
“Ɗaya daga cikin kowanne mutum uku zuwa huɗu bakar fata a duniya ɗan Nijeriya ne. Kuma nan da 2050, Nijeriya za ta kasance ƙasa ta uku mafi yawan jama’a a duniya, bayan Amurka,” in ji Shettima.
Mataimakin shugaban Ƙasa ya kuma jaddada muhimmancin rawar da masu hijira ke takawa wajen gina al’umma da haɓakar tattalin arziki. Ya tabbatar da jajircewar gwamnatin Najeriya wajen kare haƙƙin masu hijira da kuma girmama gudunmawar da suke bayarwa wajen cigaban ƙasa.
Tun a shekarar 2022, Badenoch, wacce ‘yar asalin Nijeriya kuma memba a majalisar dokokin Birtaniya, ta zargi ‘yan siyasar Nijeriya da amfani da dukiyar jama’a wajen biyan buƙatunsu na ƙashin kai. Bayan nasararta a matsayin shugabar jam’iyyar Conservative ta Birtaniya a watan Nuwamba 2024, shugabar hukumar Kula da ‘yan Nijeriya mazauna ƙetare (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta ce ofishinta ya tuntuɓi Badenoch amma ba a samu amsa ba.