Shettima ya cancanci zama Mataimakin Shugaban Ƙasa – Ganduje

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Kano, Umar Andullahi Ganduje ya ce, zaɓen Kashim Shettima a matsayin mataimaki da Bola Tinubu ya yi, ya yi daidai domin kuwa ya cancanta.

Ganduje ya bayyana hakan ne cikin sanarwar da ya fitar ta hannun Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano, Malam Muhammad Garba don taya Shettima murnar ɗauko shi da Tinubu ya yi.

Gwamnan ya ce, lallai Shettima ya cancanci wannan matsayi kuma a shirye yake ya yi aiki daidai da ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Ganduje ya ce yana da ƙwarin gwiwa kan Shettima kasancewarsa Sanatan Borno ta Tsakiya kuma tsohon gwamnan Borno.

Daga nan, ya yaba wa ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu bisa farar dabarar da ya yi na ɗaukar Shettima a matsayin abokin takara a zaɓen baɗi.

Sannan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya, musamman ‘yan Jam’iyyar APC, da su tallata ‘yan takarar don cim ma nasara a ƙarssen lamari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *