Shettima ya halarci taron ƙasashe masu albarkatun iskar gas na 2024

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Laraba ne Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima Shettima ya halarci taron ƙasa-da-ƙasa na Ƙasashe Masu Samarwa da fitar da Albarkatun Iskar gas (SIREXE) da aka gudanar a Abidjan, babban birnin ƙasar Côte D’Ivoire.

A yayin taron ne, Mataimakin shugaban ƙasar ya yi kira da a ƙarfafa harkokin shugabanci da adalci da kuma haɗin-gwiwa tsakanin shugabanni da jagororin masana’antu don samar da ci-gaba mai ɗorewa a ɓangarorin daban-daban na albarkatun Afirka.

Ya kuma jaddada ƙoƙarin da Gwamnatin Nijeriya ke yi wajen samar da Masana’antar tace albarkatun iskar gas da za ta bai wa ƙasashen maƙota damar shigowa a dama da su bisa adalci da kuma ingantawa a mataki na ƙasa.

Taken taron shine ‘Policies and Strategies for the Sustainable Development of the Extractive and Energy Industries’, wanda an samar da shi ne don haɗe kan shugabannin ƙasashen Afirka saboda tattaunawa game da amfani da hanyoyin zamani na gudanar da albarkatu da samar da tsaro wa harkar gas.