

Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Litinin ne Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya nanata aniyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sauye-sauye a harkar tattali, waɗanda za su taimaka wa bunƙasa ɓangaren gami da wadata ƙasar.
Haka kuma ya ƙaddamar da kwamitin Shugaban ƙasa kan tattali da yalwata kuɗaɗe (preCEFI) a matsayin wani ɓangare na cimma samun haɓakar tattali da zai kai na kwatankwacin dala-tiriliyan nan da shekarar 2030.
Haka ma an ƙulla yarjejeniya da masu-ruwa-da-tsaki kan masana’antu masu zaman kansu ta yadda za a samar masu da cikakken kayan aiki don gudanar da harkokinsu cikin inganci a ƙarƙashin shirin ‘Aso Accord’.
An ƙaddamar da Aso Accord ne a watan Afrilun 2024, wanda ginshiƙi ne na Ajandar Sabonta ƙasa ta gwamantin Shugaba Tinubu.

A lokacin da ya ke jawabi a taron, Shettima ya yi kira ga masu-ruwa-da-tsaki da su tallafa wa ƙoƙarin gwamnati na wadata miliyoyin al’ummar Nijeriya.
A wata sanarwa da babban mai taimaka wa Shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha ya fitar, Mataimakin Shugaban ƙasar ya ce cimma manufofin tattalin arziƙin Nijeriya suna da buƙatar aiki tuƙuru da jajircewa gami da samar da tsare-tsare masu kyau da za su taimaka wajen kai ga samun nasara.
Ya ƙara da cewa, sabon kwamitin zai yi aiki ne ta kwamitin shugabanci (GovCo) da kwamitin gudanarwa (TechCo) da taimakon sakatariyar aiwatarwa.
Kazalika ya ce kwamitin zai taimaka wajen rage matsaloli da matasa da mata da masu ƙananan sana’o’i suke fuskanta a harkokinsu na yau da kullum.
