Mataimakin shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya yi kira ga babban bankin Nijeriya (CBN) da bankunan kasuwanci su gaggauta magance matsalolin ƙarancin kuɗi da kuma cajin POS da ‘yan Nijeriya ke ƙorafi akai. Shettima ya bayyana hakan yayin jawabi a taron shekara-shekara na kwamitin bankuna da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a.
An wakilce shi ne ta mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tattalin arziki Dakta Tope Fasua, wanda ya ce, “Wannan dama ce ta roƙon ku da ku kawo ƙarshen matsalolin da ke shafar ƙoƙarin gwamnati na haɗa kowa da tsarin kuɗi da tattalin arziki.”
Mataimakin shugaban Ƙasa ya nuna damuwa kan yadda jama’a ke ƙorafin rashin samun kuɗi na ainihi da ake buƙata, tare da caccakar masu amfani da POS na titi kan caji mai tsada da rashin tsari. Ya ce, “‘yan Nijeriya suna kukan cewa ba za su iya samun kuɗin da suke buƙata ba cikin lokaci. Har ila yau, akwai matsalolin almubazzaranci daga masu POS. Muna da yaƙinin cewa za ku iya shawo kan wannan matsala.”
A jawabinsa, Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa tattalin arzikin ƙasar yana cikin matsala mai tsanani wadda aka gada daga baya. Ya ce, “Tsawon shekaru takwas zuwa tara da suka gabata, tattalin arziki ya ƙaru da kashi 1.8 cikin 100 a shekara, yayin da kuɗin da ke yawo a ƙasa ya ƙaru da kashi 13 cikin 100. Wannan yanayi ya tilasta buƙatar matakan da suka dace da girman matsalolin.”
Cardoso ya ƙara da cewa ya zama dole a samar da yanayin da zai tallafa wa ƙirƙire-ƙirƙire da ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.
Ya yi kira ga kwamitin bankuna su sake tunani kan hanyoyin da za su gina tsarin tattalin arziki mai haɗa kowa don magance matsalolin da ke addabar ƙasar da samar da mafita mai ɗorewa.