Shettima ya yi jimamin hatsarin da ya rutsa da sabbin ɗaliban da aka yaye a Jami’ar Borno

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya bayyana kaɗuwarsa game da mummunan hatsarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu ɗaliban da aka yaye a Jami’ar Borno.

Lamarin ya auku ne a Maiduguri babban birnin jihar inda ya kuma raunata wasu da dama.

Cikin wani saƙon ta’aziyya da mataimakin shugaban ƙasar ya aika a ranar Alhamis, ya yi jimamin yadda ɗaliban suka rasa damar cigaba da rayuwa bayan kammala karatu.

Ya ce rasa rayukan da aka yi ba ga iyalansu bane kaɗai, har ma da Jihar Borno da Nijeriya baki ɗaya ƙasancewar sun bar giɓin da ba za a iya cikewa ba.

Ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan mamatan da kuma jajenta wa na waɗanda suka samu raunuka gami da musu fatan samun waraka.

Shettima ya kuma tabbatar da cewa, Gwamnatin Tarayya da ta Borno za su bada duk wani agaji da taimako ake buƙata ga lamarin.

Daga ƙarshe, Shettima ya yi alƙawarin cewa Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba za ta bari irin haka ya cigaba da nakasa al’umma ba, ya na mai fatan Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu.