Shigar ƙananan yara zanga-zanga: Bayan tiya akwai wata caca!

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A daidai lokacin da nake wannan rubutu kimanin yara 150 da aka tsare su bisa zarge-zargen cin amanar ƙasa, hannu cikin yunƙurin ɓarnatar da dukiya, da tayar da hankali, waɗanda aka kama su a Abuja, Kaduna, Gombe, Jos, Katsina, da Kano yayin zanga-zangar yunwa da rashin kyakkyawan shugabanci a ƙasa da aka gudanar a watan Agusta, sun koma gaban iyayensu, bayan da wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke zarge-zargen da ake yi musu.

Sannan kuma tun kafin a yi haka, a ranar Litinin, Shugaban ƙasa ta bakin ministan watsa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, kai-tsaye ta kafafen watsa labarai na dukkan ƙasa bakiɗaya, ya sanar da cewa a mayar da dukka yaran da ake tsare da su, ba tare da wani sharaɗi ba, kuma a gudanar da bincike domin gano jami’an da suke da hannu wajen gallaza musu da cin zarafinsu, a tsawon watannin da ake tsare da su.

Babu shakka wannan al’amari ya yi matuƙar faranta ran iyayen waɗannan yara da gwamnonin jihohinsu, har ma da ɗaukacin ’yan Nijeriya. Duk wani mai nazari kan abubuwan da ke faruwa a zaurukan sada zumunta, ya ga yadda aka yi ta rubuce-rubuce, daga ’yan Arewa har zuwa ’yan Kudu, waɗanda ma ba Musulmi ba, saboda zaluncin da suke ganin an yi wajen tsare waɗannan yara da gurfanar da su a gaban kotu, cikin wani mummunan yanayi. Ciki har da rubuce-rubuce da bidiyo na tozarci ga ’yan Arewa, da irin rayuwarsu ta rashin tsari da sakaci, kamar yadda wasu mazauna kudancin ƙasar nan ke kallon ’yan Arewa.

Idan za a iya tunawa a ranar Juma’a da ta gabata, ɗaya ga watan Nuwamba ne aka gurfanar da waɗannan yara su 150 da wasu manya, bisa zargin sun shiga zanga- zangar nuna fushi kan tsadar rayuwa da aka gudanar cikin watan Agusta, inda wasu suka riƙa fashe-fashe da ƙone-ƙonen kayan gwamnati da na jama’a, wasu kuma suka riƙa ɗaga tutar ƙasar Rasha. Abin da ya fi ɗaga hankalin ’yan Nijeriya da dama, musamman ’yan Arewa, shi ne yanayin da aka fito da yaran, cikin mummunar kama. Yawancinsu duk sun fara fita a hayyacinsu saboda yunwa da azaba, ƙasusuwan haƙarƙarinsu da fuskokinsu duk sun fito, abin gwanin ban tausayi. Wasu ma har faɗuwa suka riƙa yi jikinsu ba ƙarfi, kamar sun yi kwana da kwanaki babu wanka, sun bushe sun yagalgale, saboda rashin kulawa.

‘Yan Nijeriya da dama sun zubar da hawaye saboda tausayawa, musamman iyaye waɗanda ke da yara a cikinsu, ko kuma dai suke tausayawa halin da suka ga yaran wasu a ciki. Sannan wannan abu da aka danganta da abin kunya mafi girma a Arewa, wanda wannan gwamnati  da jami’anta suka haddasa, zai jima ba a manta da shi ba. Duk kuwa da kasancewar manyan Arewa masu faɗa a ji a cikin gwamnati da wajenta sun yi ƙoƙari wajen sa baki don ganin an saki waɗannan yara, da a farko alƙalin da ya saurari tuhumar da ake yi musu, ya ce sai an ba da Naira Miliyan 10 ga kowannensu da kiyaye wasu sharuɗɗa kafin a ba da belinsu. Duk kuwa da kasancewar akasarinsu ‘ya’yan talakawa ne, ga kuma ƙuncin da ake ciki na tsadar rayuwa. Wasu iyayen ma ba su iya samu sun je sun halarci zaman sauraron tuhumar da ake yi musu a kotu ba, saboda rashin kuɗin mota daga garuruwan da suke.

Sakamakon ɓacin rai kan wannan al’amari, an rawaito cewa fitaccen ɗan gwagwarmayar kare haƙƙoƙin ɗan adam ɗin nan, mai tashar rediyo da talabijin ta Berekete Family, Ahmed Isah, ya sanar da aniyarsa ta dakatar da gabatar da shirye-shirye a tagwayen tashoshin nasa, matuƙar ba a saki yaran da aka tsare ba. Akwai wasu lauyoyi daban-daban da ke kare haƙƙoƙin raunana waɗanda su ma suka yi ruwa da tsaki cikin batun samar wa yaran kariya a gaban shari’a da tsare musu haƙƙoƙinsu, waɗanda akasarinsu ma ba ‘yan Arewa ba ne irinsu Babban Lauyan ƙasa (SAN) Wahab Shittu, Joseph Otteh, Barista Abba Hikima. Akwai kuma ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin ɗan adam irinsu Amnesty International, SERAP, NHRC, Moɓement for the Transformation of Nigeria (MOTiON) da sauransu.

Lauyoyin sun bayyana cewa, tun da farko ma kama yaran karya doka ne, suna masu kafa hujja da Dokar Kare Haƙƙoƙin Yara ta 211 sakin layi na (b) da ya hana kotu ko ‘yansanda tsare yara ƙanana, sai a inda aka same su da hannu wajen cutar da rayuwar wasu. Haka kuma sun yi bayanin cewa, kundin hukunta manyan laifuka na 2015 bai ba wa kotu damar tsare waɗanda ake zargi da laifi har na tsawon watanni biyu ba, kamar yadda aka yi wa waɗannan yara. Sashi na 296 na Kundin Hukunta Laifuka bai amince a tsare waɗanda ake zargi har fiye da kwanaki 14 ba.

A cewar, Injiniya Yakubu Isa Aljasawi, wani mai sharhi kan harkokin yau da kullum, ya bayyana takaicinsa da halin ko’in’kula da wasu ‘yan Arewa suka nuna kan al’amarin da ya faru.
Yayin da ya ƙalubalanci jami’an tsaro da suka tsare waɗannan yara masu yawa haka, bisa zargin ɗaga tutar Rasha a lokacin zanga zangar. A cewarsa, ‘ Yaushe ɗaga tutar wata ƙasa a cikin Nijeriya ya taɓa zama laifi a kundin tsarin mulkin Nijeriya? Ga mutane nan ana gani suna ɗaga tutar Biyafara da Isra’ila, da masu ɗaga tutar Saudiyya ko ta Falasɗinu, duk ba a kama su da laifin ɗaga tuta ko cin amanar ƙasa ba, sai waɗannan yaran da yawancinsu ma ba su san mene ne ɗaga tutar ke nufi ba’.

Kawo yanzu dai abin da ya faru ya riga ya faru, an tsare yara kuma Shugaban ƙasa da Babbar Kotun Tarayya sun wanke su daga duk wani laifi da ake tuhumarsu. Mun kuma ga yadda Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shattima ya jagoranci miƙa yaran ga gwamnonin jihohinsu, waɗanda su kuma suka yi alƙawarin mayar da su hannun iyayensu, bayan an binciki ingancin lafiyarsu. Kuma kamar yadda Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya faɗa a jawabinsa, Shugaba Bola Tinubu ya yi abin a yaba, bisa yadda ya saurari koke-koken jama’a, ya kuma ba da umarnin gaggawa don a saki yaran, tare da gudanar da bincike domin a hukunta jami’an da ke da hannu wajen cin zarafin yaran da tauye musu hakki na ’yan adamtaka.

Lallai ne a jinjina masa, kuma a yabawa duk waɗanda suka sa baki ta hanyoyi daban-daban wajen la’antar abubuwan da suka faru, da taimakawa wajen sakinsu. Sai dai ba zai yiwu a kashe maganar a nan ba, dole ne duk wasu da aka kama aka tsare bisa tuhumar sun shiga zanga-zanga su ma a sake su, domin hakkinsu ne ma ‘yan ƙasa su nuna damuwa kan halin da ƙasa ke ciki, duk da ba ma goyon bayan tayar da tarzoma da ɓarnatar da dukiya. Sannan ya zama wajibi a tabbatar an zaƙulo duk masu hannu wajen kama ƙananan yara da azabtar da su ko munana musu saboda zargin da ake yi musu. Kuma bayan haka a nunawa duniya irin matakin da aka ɗauka a kansu, don ya zama darasi ga ’yan baya.

Harwayau, ya kamata gwamnati ta biya iyayen waɗannan yara diyya kan halin da aka jefa su da yaransu, kuma a samar da wani tsari da zai inganta rayuwar yaran, don kada abubuwan da suka faru da su haifar musu da matsala a tunaninsu da halayyarsu. Dole ne a mayar da hankali wajen ganin rayuwarsu ba ta jirkita ko ta canza ba. A yayin da nake ganin bai dace a mayar da abin da ya faru ya zama siyasa ba, ko rabuwar kai tsakanin Arewa da Kudu ba. Amma lallai a cigaba da sanya ido, kan irin makirci da ƙulle-ƙullen da ake shiryawa Arewa da al’ummarta. Sannan ya kamata ‘yan Arewa mu yi wa kanmu karatun ta natsu, mu riƙa sanin ciwon kanmu, mu yi aiki da hankali, don ganin ba mu zubar da kima da darajar kanmu ba. A daina yi mana kallon wawaye marasa kishin kanmu da ‘yan’uwanmu.

Garemu iyaye, lallai mu ƙara mayar da hankali kan al’amarin tarbiyyar yaranmu, mu daina ƙyale yara suna galantoyi a titi ko suna shiga hayaniyar unguwa ko tarzoma, bisa la’akari da abubuwan da suka faru da waɗannan yara. Da halin da muke gani na yadda faɗace-faɗecen Daba ya jefa Kano da wasu garuruwan Arewa cikin barazanar tsaro, da lalacewar tarbiyya.

Allah Ya shirya mana zuriya bakiɗaya.