Shigar Nijeriya hidimar yaƙi a Nijar: A yi hattara ko a sha kunya

Bayanan da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ke Yi da Nijeriya da ECOWAS na shirin kai hari wa sojojin Nijar, babbar kasada ce kowa ya iya allonsa ya wanke su ji da matsalar Zamfara da matsalar yunwa da boren da talakawa ke shirin shiga.

Sun fi kowa sanin ba a raina yaƙi su tambayi Rasha a Ukraine yadda wanki ya Kai su dare kowane gefe ke asarar soja da dukiya. Sojojin Nijar ba kanwar lasa bane idan suka yi wannan kuskure kafin su kai Maradi ko Tahwa kan hanyar zuwa Niamey karon ba zai musu daɗi ba.

Saboda na shiga Nijar shekaru shida da suka wuce ta Dan Isa naje Zinder na wuce Diffa lokacin yakin Boko Haram don ganewa idona halin da ‘yan gudun Hijrar mu ke ciki.

Ƙungiyar Redcross sun buƙaci na koma ta inda na fito a Katsina don ’yan Boko Haram suna kawo hari ko yaushe. Kuma lokacin ne suka ƙona Gaidem. Amma nace da su idan akwai masu wucewa zan bi su insha Allah zan wuce. Haka na shiga Mota zuwa Gaidem na iso ƙarfe biyar lokacin rufe yankin don haka ake ruruwar komawa cikin daji ko garin Maine Saroa Nijar a kwana da safe a dawo Gaidem don Boko Haram suna kawo hari ko yaushe.

Ina ƙoƙarin neman ayari don tafiya kwana a daji sai ga motar Yobe Line na hau nazo Gashuwa na kwana daga Nan na dawo Potiskum zuwa Bauchi.

Idan ka ga yadda sojojin Nijar ke Patrol daga Diffa zuwa kan iyakar Nijar ɗauke da manyan makamai Kai kace za a ƙone ko ina a kan iyakokin. Amma da na shigo Nijeriya sai na ga sojojin mu ɗauke da bindigogi AK 47 a Hilux tsoffin suna patrol wallahi sai naji tausayin su.

Kuma a ba a jima ba a kan iyakar Geidam aka kashe Immigration da sojoji masu yawa a lokacin da Boko Haram suka kawo musu farmaki. Don haka sojojin Nijeriya su yi hattara kada su biye Yan siyasa su jefa ƙasar mu cikin sabon yaqi bayan fitina daban-daban da muke ciki. Allah ya mana maganin abin da ya fi ƙarfin mu.

Daga Muazu Hardawa Edita Jaridar Alheri reporter Dandalkura radio Bauchi.08062333065.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *