Shigowar gwamnati da ‘yan kasuwa zai kawo bunƙasar rubutun adabi – Shamsiyya Manga

Marubuta ku tsaftace alƙalaminku ko don goben ku ta yi kyau”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Cigaba da tumbatsar da ake samu ta marubuta a kafafen sadarwa na zamani, bai hana waɗanda suka yi fice kuma suka goge da sha’anin rubutu, samun nasarori da ɗaukaka ba. Wasu marubuta na ganin yawan masu rubutu a onlayin ba ya hana su samun masoya da masu bibiyar littattafansu, duk kuwa da cewa da ake yi, idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai. Shamsiyya Usman Manga, na daga cikin matasan marubuta da tauraruwarsu ke haskawa. Kuma bayan kasancewarta marubuciya har wa yau Ungozoma ce da ke aiki a Asibitin Ƙwararru na Jihar Yobe da ke Potiskum. Sai dai duk da ɗawainiyar aikin asibiti, Shamsiyya ta ce aikinta ba ya hana ta rubutu, don shi ne abin da ya fi xebe mata kewa. A zantawarta da wakilin Manhaja Blueprint, Abba Abubakar Yakubu, ya tattauna da baƙuwar mu ta wannan mako.

MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki, wacce ce Shamsiyya Manga?

SHAMSIYYA: Salamu Alaikum. Ni asalin sunana shi ne, Shamsiyya Usman Manga, amma a duniyar marubuta na fi amfani da Shamsiyya Manga kawai. Ni marubuciyar onlayin ce, sannan ma’aikaciyar lafiya.

Ba mu taƙaitaccen tarihin rayuwarki.

An haife ni a Jihar Yobe a Ƙaramar Hukumar Potiskum. Na yi karatu tun daga matakin firamare har zuwa sakandire, duk a cikin garin Potiskum. Daga baya na tafi Kwalejin Horar da Masu Aikin Jinya Da Ungozoma da ke Birnin Kudu a Jihar Jigawa yanzu haka ina aiki a Asibitin ƙwararru na Jihar Yobe da ke a garin Potiskum a matsayin Ungozoma, wato Midwife.

Menene ya ba ki sha’awa ki ka fara rubutun littattafan Hausa?

Abin da ya bani sha’awa har na fara rubutun littafin Hausa shi ne gaskiya na taso ina son rubutu a cikin zuciyata. Sannan marubuta suna burge ni sosai, hakan ya sanya tun ina sakandire nake yawan karance-karance amma kuma nafi karatun littattafan tarihi da kuma na yaƙi. Hakan ya sa nake jin ina ma nima zan zama ɗaya daga cikin waɗannan mutanen, domin a gaskiya na ɗauki marubuta wasu mutane na daban waɗanda nake musu kallo ba irin sauran mutane ba. Ban taɓa tsammanin zan zama marubuciya ba, sai dai kuma shi abin da Allah Ya tsarawa bawa to, ba makawa sai ya faru. A cikin ikon Allah yau gani a duniyar marubuta, ni ma ana damawa da ni.

Kawo yanzu kin rubuta littattafai sun kai nawa, sannan ki kawo wani taƙaitaccen bayani kan wasu fitattu uku daga ciki?

Na rubuta littattafai za su kai guda shida zuwa bakwai har da gajerun labarai da nake rubutawa ina ajiyewa. Daga ciki akwai ‘Sadiq ɗan Dako Ne’, ‘Wata Ƙaddara’, Fansar Fatalwa’, ‘Ƙalubalen Rayuwa’. Yaqin Mata’, sai kuma ‘Matan Zamani’, da nake kan aikin shi yanzu wanda zai fito nan da bayan sallar layya in sha Allah.

Kamar shi littafina na farko shi ne, Sadiq ɗan Dako Ne’, labari ne da ya ƙunshi irin rayuwar da mu ke fuskanta ta yadda wasu masu kuɗi suke ƙyamatar talakawa, inda daga baya kuma waɗannan da suka raina ɗin sai su zo su zame musu ciwon ido. Labarin ya yi nuni ne a kan wani matashin saurayi ɗan dako wanda yake faɗi tashi wajen ganin ya rufa wa kansa da iyayensa asiri. A ɗaya vangaren kuma akwai Alhaji Bukar yana da ‘ya Mufeeda wadda halin su ya bambanta, ita tana son talaka shi kuma mahaifinta idan akwai babban maƙiyin shi a duniya to, talaka ne. Hakan ya sanya ta faɗa soyayya da shi Sadiq ɗan dako inda daga ƙarshe rabo ya rantse har ya kai su ga aure, sai dai mahaifin ta Alhaji Bukar ya ɗauki alwashin raba auren.

Sai littafin ‘Wata Ƙaddara, shi kuma labari ne a kan wani shahararren mai kuɗi wanda sata ita ce sana’ar shi wadda tun yana ɗan ƙarami ya addabi mutanen garinsu da sata wannan ya yi sanadiyar mutuwar mahaifiyarsa kuma a dalilin haka mahaifinsa ya haukace ya bi duniya ba a san inda yake ba. Bayan ya girma sai abin na sa ya shaharadomin har ƙungiya gare su ta shahararrun ɓarayi hakan ta sanya har ya mallakawa dodon tsafin su ‘yarsa mai suna Ramlat, saboda kawai neman shahara da ɗaukaka inda yarinyar ta tashi a kangare har ta auri miji wanda yake salihi, sai dai kuma halin ɓeran da yake nuna mishi ya sa ya saketa wanda shi ya zamo silar tonon asirin mahaifinta.

Akwai kuma littafina ‘Fansar Fatalwa’, shi kuma labari ne akan wasu aminan juna guda biyar Amrah, Afrah, Azrah, Amirah, da kuma Anisa waɗanda hassada da son zuciya ta kai su ga haɗa baki su ci amanar ɗaya daga cikin su mai suna Amrah, inda suka ɗauki bidiyon tsaraicinta suka yaɗa a duniya wannan ya zamo silar rabuwarta da saurayin ta wanda aka musu baiko da shi ya koma soyayya da ɗaya daga cikin ƙawayen ta mai suna Afrah. A ɗaya ɓangaren kuma hakan ya tava rayuwarta har ya yi sanadiyar mutuwarta da ita da yayanta, inda daga baya kuma ta dawo ɗaukar fansa a matsayin fatalwa, ta bi su ɗaya bayan ɗaya tana musu kisan wulaƙanci.

Yaya ki ke fahimtar yadda masu karatun littattafanki suke jin daɗin rubutunki?

Idan na yi fitar da littafi na ga ana sharhi sosai, sannan kuma idan na ga suna yawan min magana ta private to, hakan yana sa na fahimci cewar saƙona ya isa kuma sun ji daɗin sa. Ni kuma wannan ya na faranta min rai sosai, kuma ina jin daɗi matuƙa.

Ganin yadda aka samu yawaitar marubuta a online, shin yaya kasuwancin littattafan ke tafiya?

To, Alhamdulillahi. Ita gaskiya kasuwa daman yau idan ta maka daɗi ne to, gobe ta waninka ce, musamman a onlayin. Yadda marubuta suka yawaita to, dole littattafan wasu za su fi na wasu karɓuwa. Duk da cewar marubuta online suna fuskantar ƙalubale wajen fitar musu da littafi da masu karatu suke yi. Wannan ya kan jawo raguwar masu sayen littafin. Tun da wani zai ce ga na bati mai zai sa ya cire kuɗi ya saya.

Shin kina samun alheri da rubutun da ki ke yi, ko dai sha’awa ce ta sa ki ke cigaba da yi?

Ƙwarai kuwa, ina samun alheri sosai. Sai dai mu ce Alhamdulillahi, don ko iya addu’ar da masoyanka suke ma ita kaɗai ta wadatar. Sannan da yake ina son rubutun a cikin zuciyata wannan ya sa nake ji idan ba wani babban dalili ba to, ba zan iya barin harkar rubutu ba.

Yaya ki ke ganin za a inganta cigaban harkar rubutun adabi a ƙasar nan?

Ta hanyar shigowar gwamnati da masu ruwa da tsaki a cikin marubuta, domin su riƙa tallafa musu, sannan a yawaita ƙirƙirar gasanni a tsakanin marubuta kamar yadda BBC Hausa suke sanya Gasar Hikayata da kuma irin su Gusau Institute to, hakan zai taimaka sosai wajen inganta harkar rubutun adabin. Sannan a samu editoci waɗanda za su riƙa sharhi a kan littattafan marubuta, hakan zai ƙara inganta rubutun adabin sosai.

Duba da irin aikin da ki ke yi, wanne lokaci ki ka fi samun damar yin rubutu?

Gaskiya nafi samun damar yin rubutu a lokacin da bani da aiki, misali idan ina aikin rana to, da safe nake yin rubutu. Idan ina aikin safe kuma da rana nake rubutu, in kuma aikin kwana nake da shi sai bayan na dawo da safe na yi bacci na tashi tsakanin azahar da la’asar sai na yi.

Yaya ki ke kallon irin zumuncin da ke tsakanin marubutan online, yaya ku ke sanin junanku?

Akwai zumunci mai ƙarfi sosai tsakanin marubuta na onlayin duba da cewar akwai zauruka daban daban da ake buɗewa na marubuta zalla to, hakan ya kan taimaka wajen ƙara inganta zumunci a tsakanin marubutan.

A cikin marubutan online su waye ku ka fi samun fahimtar juna, kuma me ya sa?

Ni gaskiya yawanci waɗanda mu ke mu’amala da su akwai fahimtar juna sosai a tsakanin mu. Wasu ma ni na ɗauke su tamkar Yayuna, wasu kuma ƙawaye na. Misali, akwai marubutan da a ko’ina zan shaida su saboda karamcin su a gare ni da kuma sauƙin kan su, irin su yayata Hadiza D. Auta, Anti Binta Umar, Amira Adam, Oum Nass, Ummi Garkuwa da sauran su.

A ɓangaren maza kuma akwai irin su Abdallah Hassan Yarima, Muttaka Hassan, Jamil Nafseen, Abba Abubakar, sai ƙawaye na irin su Milhaty watau Fadila Yakubu, Amina Ƴandoma, Lailat, Queen Nasmah, Asma’u Jasmine, R. Hussain wadda aka fi sani da Zinariyar Royal, Aisha D. Fulani, da duk wanda nake mu’amala da shi a cikin marubuta. Ina matuqar jin daɗin kasancewata tare da marubuta, saboda su mutane ne masu karamci. Muna girmama juna, kuma muna kare mutuncin juna.

Wacce gudunmawa ki ke ganin tsofaffin marubuta za su bai wa matasan da ke vangaren online, don a samu bunƙasa harkar adabin Hausa?

Su zama masu taimaka musu suna jan su a jiki, idan sun ga gyara su gyara musu, idan sun yi kuskure a gyara musu. Kai kuma a matsayinkana sabon marubuci, idan aka maka gyara sai ka karɓa ka yi godiya.

Kina ganin shigowar gwamnati zai taimaka wajen tsaftace harkar rubutun adabi daga masu ɓata harkar?

Sosai ma kuwa musamman jami’an tsaro da hukumomi irin su Hisbah, duk wadda take yin rubutu na ɓata tarbiyya a kaita a ladabtar da ita. Tun da na lura irin su basa jin shawara, kuma basa ɗaukar wa’azi to, amma wataƙila idan an hada da hukuma ko Gwamnati abin zai iya raguwa.

Wanne abu ne ya tava faruwa da ke a sanadiyyar rubutu, wanda ba za ki manta da shi ba?

Gasa da na tava ci ta zauren marubuta wanda ban tava tsammanin zan ci ba, sai ga shi Alhamdulillahi bugu ɗaya an wuce wajen, wanda na san hakan ba iyawata ba ce, ba kuma dabara ta ba ce, nufi ne na Ubangiji. Wannan abin ba zan tava mantawa da shi ba gaskiya.

Wanne ƙalubale ki ke fuskanta a harkar rubutun adabi tun da ki ka fara?

Akwai wani abu da ya taɓa faruwa lokacin ina rubuta littafina na Fansar Fatalwa’, wanda sai da na yi kuka kuma na ji kamar na dakata da rubuta labarin. Cikin ikon Allah kuma sai gashi labarin shi ya zamo sanadin ɗaukaka ta domin kuwa labarin ya karɓu yadda ban yi zato ba.

Gaya mana wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma wanne tasiri ƙungiyoyin marubuta suke da shi ga cigaban mambobinsu?

Ni cikakkiyar mamba ce a ƙungiyar marubuta ta Manazarta Writers Association. Kuma na yarda akwai tasiri sosai da ƙungiya ke da shi musamman ga mambobinsu, kamar ta wajen gyaran ƙa’idojin rubutu, saboda yawanci waɗanda suke da ƙungiya ba su cika yin rubutu kara zube ba, ana gyara musu, savanin waɗanda ba su da ƙungiya. Sannan ko satar fasaha da ake yi nan ma idan kana da ƙungiya abin zai zo maka da sauƙi, saboda ƙungiyar ka za ta iya tsaya maka kai da fata wajen ganin an bi maka haƙƙinka.

Wacce shawara ki ke da ita ga sauran marubuta bakiɗaya?

Shawarata ga marubuta shi ne su zama masu tsaftace alƙalaminsu saboda goben su ta yi kyau, sannan su zama masu haɗin kai.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?

Zakaran Da Allah Ya Nufa Da Cara…

Muna godiya.

Ni ce da godiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *