Shin ana sane ake bawa ‘yan shaye-shaye mafaka a gwamnatance da siyasance?

Daga AMB. AUWAL MUHAMMAD ƊANLARABAWA

Ni Amb Auwal Muhd Ɗanlarabawa, ina kira a kan shugabanni da hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a kan a kawo ɗauki wuraren da ake shaye-shaye kamar sakatariyar ƙananan hukumomi da ma’aikatun gwamnati da sauran wuraren taruwar ‘yan siyasa don magance ta’ammali da kayan maye.

Ni a ganina, da yawa ana kokawa da yadda matasa ke amfani ma’aikatun Gwamnati da wuraren da ake hada-hadar siyasa tare da fakewa ana shaye-shaye, wanda ba mai hanawa ballantana saka doka ta hana su cigaba da aikata laifuka.

Hakazalika, Masu kawo ƙorafi sun bayyana cewa idan aka je sakatariyar da ake da su a ƙananan hukumomi ana tarar da dandazon matasa waɗanda ke ta’ammali da kayan maye da shaye-shaye da sauran wuraren da ake sabgogin siyasa da wasu ma’aikatu na Gwamnati.

Shin abin tambaya a nan shi ne, hukumar da ke yaƙi da shaye-shaye bata san da waɗannan wuraren ba ne? Ko su an cire su daga jerin wuraren da ba a Kama ‘yan shaye-shaye a wurin an basu lasisin cigaba da aikata laifukan ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da wiwi da sauransu?

A ƙarshe, ina kira ga al’umma da wannan hukuma cewar ta samar da wani tsari wanda zai hana yin anfani da wurare da za a taru don yin shaye-shaye a kowacce unguwa, kamar ramuka, kangwaye, gidajen Kallo, cinema, gidan gala gidan dambe, da sauransu, hakan zai taimaka sosai wajen daƙilewa da kuma hana yawaitar matasa ‘yan shaye-shaye a unguwanni da ma gari bakiɗaya.

Amb. Auwal Muhd Ɗanlarabawa shi ne Shugaban gidauniyar tallafa wa mabuwata daga tushe (Grassroot Care and Aid Foundation) Kano, Nijeriya.