Tare Da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Zan fara da batun Godwin Emefiele kafin shiga batun tsadar rayuwa. Haƙiƙa a ’yan kwanaki biyun nan labarun yadda ta kaya a kotun Legas kan dakataccen gwamnan babbban banki Godwin Emefiele ya zama kan gaba a kafafe. Ba kotu kaɗai ce ta buƙaci ko umurci ’yan sandan farin kaya DSS ssu sake Emefiele ko su gurfanar da shi gaban kotu. DSS ta cimma umurnin kotun don maimakon ta sake Emefiele ta zaɓi gurfanar da shi gaban kotu ne don fara cajin da da dalilan kama shi fiye da wata ɗaya da ya wuce.
Rundunar farin kaya ta DSS ta sake cafke dakataccen gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele bayan samun belin da ya yi a babbar kotun taraiya da ke Legas.
Mai shari’a Nicholas Oweibo ya ba da belin Emeiele bisa cajin da a ka yi ma sa na mallakar bindiga da albarusai ba lasisi.
Jostis Oweibo ya ce wannan laifi ko truhumar za a iya ba da belin wanda a ke tuhuma; inda ya ba da belin da umurtar tura Emefiele gidan yari har sai ya cika sharuɗɗan ba da belin da su ka haɗa da Naira miliyan ashirin da wani wanda zai tsaya ma sa shi mai darajar mallakar adadin waɗannan kuɗin.
Amma yayin da jami’an gidan yari ke shirin ɗaukar Emefiele don tafiya da shi ma’adananar su, sai jami’an DSS su ka sake cafke shi da nuna su na da takardar kotu da ta ba da izinin sake kama shi.
An samu ‘yar hatsaniya tsakanin jami’an biyu har dai DSS su ka ɗauke Emefiele.
Wannan na nuna akwai sauran magana kan cajin da DSS ke shiryawa Emefiele bisa binciken da su ka gudanar ko su ke gudanarwa.
Rundunar ta DSS ta bayyana cewa ba ta saba duk wata doka ba ga yadda ta ke tafiyar da lamuran shari’ar dakataccen gwamnan babban banki Godwin Emefiele.
Sanarwa daga daraktan labarun rundunar Peter Afunanya ta na magana ne kan hatsaniyar da ta afku wajen sake kama Emefiele tsakanin jami’an ta da na gidan yari a babbar kotun taraiya a Legas bayan Emefile ya samu beli.
Afunanya wanda ya ce a na binciken dalilan hatsaniyar da hakan bai dace ba don kuwa duk ɓangarorin biyu sun nuna zalama.
DSS ta ce za ta cigaba da aiki bisa ƙa’ida ta na mai zargin wasu mutane da neman batawa rundunar suna. Tun ma gabanin gurfanar da Emefiele gaban kotu manyan lauyoyi ke nuna mamakin cajin da a ka yi ma sa na mallakr bindiga da albarusai da su ke ganin abun mamaki ne a ce mutum kamar gwamnan babban banki a na tuhumar sa da mallakar bindiga.
Wani ma mai sharhi kan lamarin na nuna irin bindigar nan ce da uban ’yan boko Mungo Park ko baturen da ya gano Amurka Christopher Columbus su ka riƙe. Wato dai a nan irin bindigar nan ce ta mazan jiya da ma bai dace a yi magana a kan ta ba. Hakanan an ga wani lauya ma bayan fitowa daga kotu a Legas da samun hatsaniya ya fuskanci jami’an na DSS ya na mai cewa sam abun da su ka aikata ba daidai ba ne. Lauyan ya yi ikirarin cewa DSS ta yi abun kunya don kin amfani da abun da babbar kotu ta yanke maimakon haka ta kawo umurni daga kotun majistare ta neman sake kama Emefiele.
Shin takardar nan ko umurnin nan na majistare ne ko wata babbar kotun, an ga DSS sun sanya Emefiele a cikin mota sun yi awun gaba da shi. Kafin nan an ga wani jami’in gidan yari da ya jajirce sai sun tafi da Emefiele ya samu turjiya daga jami’an DSS inda su ka ingije shi da hana shi sakat wajen neman dauke wanda ya samu belin. A dai faifan bidiyon, shi kan sa Emefiele ya ce a na hayaniya a waje da alamun kuma ba ya son ya shiga cikin hayaniyar ko kuma ya fahimci lalle akwai yiwuwar jami’an DSS na son sake kama shi ne.
Haka dai a ka buƙaci Emefiele ya zauna har lamura su natsa amma daga ƙarshe dai DSS ta sake kama shi don fuskantar wasu tuhume-tuhume. Ga akasarin ’yan Nijeriya musamman talakawa ba su ga laifin sake kama Emefiele ba don su na tuno wasu manufofin Emefiele da su ka wahalar da su kamar canjin kuɗi da ya sa su ka rasa kuɗin kashewa da kwana da yunwa ko zama cikin zafin ciwo ba kuɗin sayan magani. Tuna manufofi masu wuya sun sa da yawa ba sa tausayawa halin da Emefiele ya shiga ko jera sahu da wasu lauyoyi da ke caccakar rundunar DSS da yadda ya nuna ta na duba gabatar da caji kan Emefiele daki-daki ne.
A gaskiya ba na ganin talakawa na cikin damuwa kan halin da Emefiele ya ke ciki. Mamakin dai a nan shi ne ga wanda a ke zargin ya karya tattalin arzikin ƙasa amma sai a ka fara shigar da shi ƙara kotu da tuhumar samun sa da bindiga ko albarusai da ba lasisi. Irin wannan caji kamar an kama wani dan bindiga ko mai ɗaukar nauyin ɓarayin daji.
A gefe guda kuma shari’ar Emefiele ba ta ɗauki hankali sosai ba don ƙuncin tattalin arzikin da ƙasa ke ciki sanadiyyar janye tallafin man fetur. Wayar gari da ƙara farashin fetur ya kara sanya zukatan mutane raurawa. Sabuwar barazanar afkawa yajin aikin ƙungiyar ƙwadagon Nijeriya a makon farko na Agustar nan matuƙar gwamnati ba ta kawo sauƙin rayuwa ba, na samun goyon bayan jama’a.
Barazanar ta biyo bayan barin kasuwar sayar da fetur ta yi halin ta inda ’yan kasuwa ke da hurumin kara farashi bisa yadda za su ci riba mai yawa ko dai a ce su maida kuɗi kuma su dora ribar da su ke ganin za ta fishshe su.
Malam Umar Abubakar mai sayar da shanu ne a kasuwa Abaji Abuja ya ce rayuwar masu saye da sayarwa ta na cikin damuwa don burin su ba ma samun riba ba ne yanzu “a baya mu na loda cikin motar shanu Naira dubu 25 amma yanzu mu kan biya Naira dubu 35 ahar ma fiye da hakan. Yanzu dai mu kan sayar da shanun ne kawai mu maida kuɗi ba batun samun riba ba.”
Har yanzu dai ba a gama samun maslahar tattaunawar gwamnati da ƙungiyar ƙwadago kan biyan buƙatun qungiyar ba na inganta albashin ma’aikata da bita kan hanyoyin sauƙaƙa rayuwa don ɗan karen tsadar rayuwa da a ka samu a sanadiyyar janye tallafin fetur.
Bayan tashi daga taro, ƙungiyar ƙwadagon ta ture batun umurnin kotu na dakatar da tafiya yajin aiki a baya inda ta ba da sabon wa’adin sa kafar wando daya da gwamnatin.
Komred Nasir Kabir jami’in ƙungiyar ƙwadagon ne da ke ba da tabbacin wannan karo ƙungiyar ba za ta saurarawa daɗin baki ba “sam ba mu amince da janye tallafin fetur ba kuma ba za mu zuba ido gwamnati ta azabtar da ’yan Nijeriya ba.”
Nastura Ashir Sharif da ke matsayin shugaban amintattun ƙungiyoyin arewa ya ce tun da an mika ragamar farashin fetur hannun ’yan jari hujja sai yadda su ka dama za a sha “shugaban ƙasa ya kamata ya sani cewa ƙasar ba ta ‘yan kasuwa ne kaɗai ba, akwai talakawa akwai ragowar al’umma ’yan ƙasa, cewar a bar wasu ’yan tsiraru saboda son zuciyar su da kasuwancin su da neman abun duniyar su a ce kullum za mayar da ’yan ƙasa bayi masu tarawa waɗancan kuɗi; ba a dora qasa a kan gaskiya ba kuma abun ba zai dore ba za a wayi gari mutanen ba za su amince da abun da a ke mu su ba.” Sharif ya nuna fargabar ’yan jari hujja zuwa ƙarshen shekarar nan ka iya mayar da litar man fetur Naira 1000.
A nan mai taimakawa shugaba Tinubu kan labaru Abdul’aziz Abdul’aziz ya nuna ƙwarin gwiwar kafin ranar wa’adin yajin za a ga sauye-sauyen da gwamnati ta yi alwashi, ya na mai nanata cewa yanzu harkar fetur na hannun ‘yan kasuwa ne a tsarin kasuwa ta yi halin ta.
Kusan dukkan muhimman kayan masarufi musamman na abinci sun ninka kuɗi inda kukan ya wuce kan talakawa kaɗai har da ’yan tsaka-tsaki na cewa ba sa adana komai matuƙar za su zuba mai a tankunan motocin su. Gaskiyar magana albashin matsaikacin ma’aikaci ba zai iya ɗaukar nauyin zuba mai a mota a tsawon wata sannan canji ya rage a samu na cefane ba. Su kananan ma’aikata dama dabaru su ke yi su tafi aiki ta shiga motocin safa su kai su wajajen da za su sauka su karisa zuwa bakin aiki da sawu.
Kammalawa;
Tun watannin uku ko huɗu na ƙarshe na gwamnatin Buhari zuwa har yanzun nan da na ke rubutu labarun tangarda da matsaloli da kan wahalar da talakawa a ke samu kama daga canjin kuɗi, rag yawan kuɗin da za a iya fitarwa a banki, cire tallafin fetur, ɗan karen tsadar kayan masarufi da sauran su. Yaya za a yi da ya wuce kowa ya riƙa zama ya na tsara yadda zai gudanar da rayuwar sa a wuni da ririta dan abun da ya ke samu har ranar da Allah maɗaukakin Sarki ya kawo ma na sauƙi don haƙiƙa bayan tsanani akwai sauƙi.