Shin maƙarƙashiya aka shirya don sauke Alƙalin Alƙalai, Ibrahim Tanko?

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

A bisa ƙoƙarin toshe duk wata kafa gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekara ta 2023 musamman idan lamarin ya jiɓanci kotuna, magoya bayan ɗan takarar shugabancin ƙasa na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu suka ɗauki mataki na sunƙuru na sauke Alƙalin Alƙalai na Tarayyar Nijeriya, Ibrahim Tanko Muhammad daga kan kujerarsa ta mulki.

Kafar yaɗa labarai ta ‘Pointblanknews.com’ tun tuni a hukumance ta gano cewar, masu ilimin yin wannan yaqin sunƙuru suna son yin amfani da salon yadda aka ture tsohon Alƙalin Alƙalai na Tarayyar Nijeriya, Mai Shari’a Walter  ne, a yunƙurin su na son yin amfani da wancan salon.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewar, ɓoyayyiyar wasiƙa da ta bayyana wacce Alqalan Kotun Ƙoli su guda goma sha huɗu suka rubuta wa Mai Shari’a Ibrahim Tanko Mohammad ita ce mataki na farko na ƙoƙarin tunɓuke shi daga kujerar sa ta shugabancin masu shari’a na ƙasar nan.

Majiyar ta cigaba da cewar, wannan shiri na ƙarƙashin ƙasa da alƙalan guda 14 suke yi, har ila yau wata hanya ce ta ɗora Mai Shari’a Olukayode Ariwoola kan kujerar shugabancin idan suka yi nasarar tunɓuke tsohon Alkalin Alkalai na ƙasar nan, Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad daga kan kujerarsa ta shugabanci.

“Xabagogin shirye-shirye, kamar yadda masu ilimin janhurun suka shirya, za ta kai ga sauke tsohon Alƙalin Alƙalan daga kan kujerarsa. Kamar a batun sauke Mai Shari’a Walter Onnoghen daga kan kujerarsa, wani lamari da bai taka kara ya karya ba, zai sauke Tanko daga kan karaga.

“Wannan mataki zai shimfiɗa kyakkyawar hanya ta canja CJN Tanko da mafi kusa da shi a jerin girma, Mai Shira’a Ariwoola wanda magoya bayan Tinubu suka amince wa, koda zaven shugaban qasa na shekarar 2023 ya taho da gardama, ko ya yi masu ba-zata.

“Ta wannan hanya kenan, ba su buƙatar kai komo na neman wanda zai yi shari’a ta yadda zai cimma manufarsu ta ganin cewar, Tinubu ya kasance shugaban ƙasa, kuma buƙatar su ta biya.

Idan za a iya tunawa dai, Alƙalan guda 14 na Kotun Qoli a cikin takardar zargi da suka rubuta wa tsohon Alƙalin Alƙalai mai murabus, sun zarge shi da yin sakaci da ayyukan sa, haɗi da karkata wasu kuɗaɗe na gudanar da wasu ayyukan kotunansu.

Daga cikin batutuwa da alƙalan 14 suka gabatar sun haɗa da muhalli, motocin hawa, biyan kuɗaɗen lantarki, samar da man dizel, haɗa gidajen su da na’urorin sadarwa, horas da alkalai, da ƙarancin wutar lantarki a kotunansu.

Alƙalan 14 sun kuma zargi Alƙalin Alƙalai mai murabus da cewar, ya karɓi koke-kokensu na buƙatar zama a tattauna, tare da bibiyar batun tattaunawar na tsawon ba tare da ya amince ba, har zuwa 31 ga watan Maris da ya amince aka zauna, har ma aka kafa kwamiti na duba batun walwalar alƙalai.

A ranar Litinin ce, 27 ga watan Yuni na wannan shekara ta 2022 da ta gabata aka tilasta wa Alƙalin Alƙalai na Tarayyar Nijeriya yin ritaya, watanni 18 gabanin yin ritayarsa na wa’adin aiki, kamar yadda lokacin yin ritayarsa ta kama a watan Disamba ta shekarar 2023.

A ranar ta Litinin ɗin ce, Shugaban Qasa, Muhammad Buhar ya rantsar da Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin muqaddashin Alƙalin Alƙalai na tarayyar Nijeriya.

Tunda farkon wannan rana dai, sai da kafofin yada labarai na tarayyar Nijeriya suka tumbatsa da labarun cewar, Alƙalin Alƙalai Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad ya yi murabus bisa dalilin rashin isasshiyar lafiyar jiki.

Da yake karɓar takardar yin ritayar ta Mai Shari’a Ibrahim Tanko Muhammad wanda aka ba shi ya sanya hannu a kai, gabanin rantsar da sabon Alƙalin Alƙalan, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa mai murabus Ibrahim Tanko fatar ingancin lafiyarsa.

Olukayode Ariwoola dai, bacin mai murabus Ibrahim Tanko shine mafi girma a Kotun Ƙoli ta tarayyar Nijeriya, an haife shine a ranar 28 ga watan Agusta ta shekarar 1958, kuma ya zama Alƙali a Kotun Ƙoli ta Nijeriya a shekara ta 2011.

Kafin nan Ariwoola Mai Shari’a ne a Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayyar Nijeriya tsakanin shekarar 2005 zuwa 2011, bayan da aka ɗaukaka shi daga Babbar Kotun Jihar Oyo, bayan farkon ɗaukar sa aiki a matsayin Alƙali a jihar ta Oyo a shekarar 1992. Ana sanya ran yin ritayarsa, idan Allah ya tsawonta kwanakinsa, a shekara ta 2028.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *