Shin mayaƙan Sham tsagera ne?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ko da kuwa wani zai kira mayaƙan Hayat Tahrir Al-Sham da su ka amshi madafun ikon ƙasar Sham wato Siriya a matsayin tsagera a halin yanzu dai gwamnati na hannun su. Na ga aƙalla ɗaya daga manyan kafafen labaru a gabar ta tsakiya na zayyana su da zama tsagera wanda hakan ya sa a ke ɗari-ɗari  da su a matsayin shugabannin wannan ƙasa mai tarihi. Ba mamaki kamar yadda a kan zayyana gwamnatocin mulkin soja a wasu ƙasashen Afurka da masu mulkin kama-karya ko da ba su karya ƙasashen ba, hakan ya zama suna ga mayaka da su ka tada kayar baya har su ka cimma gaci. Matuƙar za a taimaki talakawan Sham to sai an samu zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar. Lallai ba daidai ba ne a yi ta jifar mayaƙan da sunaye har ta kai ga wasu ma sun dau makaman don tinkarar su a yi ta gwabzawa ƙasar ta afka sabuwar fitina. Fitinar gwamnatin soja ta Sudan ƙarƙashin Janar Abdelfatah Burhan da na mayaka ‘yan sa kai na Hameti Hamdan Daglo ya nemi daidaita gagarumar kasa irin Sudan. Har yau Sudan ba ta farfado ko fita daga wannan gwagwarmayar masar madafun iko ba. Kuma fitinar ta hargitsa lamuran jama’ar ƙasar. Mu duba Yaman ma yanda har yau a ke arangama tsakanin ‘yan Houthi da gwamnatin dimokraɗiyya ta birnin Aden. Har yau Houthi ke riƙe da babban birnin ƙasar Sanaa don fitinar da ta yi awun gaba da shugaban ƙƙsar Ali Abdallah Saleh wanda daga bisani ma ‘yan Houthi su ka kashe shi. Libya ma ba ta tsira bat un da fitina ta ɓarke da taimakon wasu daga ƙetare ta kai ga kisan gilla ga shugaban ƙasar Moammar Ghaddafi, har yau ƙasar ba ta dawo daidai ba don ta fada hannun mayaƙa na sassa.

Mun san dai akwai lokacin da shugaban ‘yan tawaye Khalifa Haftar ya so kifar da gwamnatin birnin Tiripoli/Durabulus. Gaskiyar magana da zarar katangar ƙasa ta tsage to kadangaru kan shiga su hana lamura dawowa daidai. Mun tuna bayan doguwar gwagwarmayar ‘yan Taliban a Afghanistan sun amshi madafun mulki amma daga bisani a ka ɓullo da wasu mayaƙan na da  sunan haɗin guiwar arewa “northern alliance” waɗanda su ka nausa birnin Kabul su ka amshe madafun iko. Sai bayan shekaru kimanin 20 ‘yan Taliban su ka samu dawowa kan karaga kuma an tafka asarar rayuka. Matukar mayaƙan Sham ba su samu haɗin kan musamman ‘yan uwan su Larabawa ba to za a cigaba da ɗaukar ƙasar na hannun tsagera ne. Yayin da mun san gwamnatin Assad na samun goyon bayan Iran ne, kai tsaye mayaƙan nan na samun goyon bayan Turkiyya ne. In mun duba duk ɓangarorin biyu ba daga ‘yan uwan su Larabawa su ke samun goyon baya ba wannan na samu daga Parisawa wannan na samu daga Turkawa. Shin Larabawa za su iya haɗa kai su marawa mayakan Sham baya don amfanin al’ummar ƙasar su huta daga yaƙin basasar da ya faro tun 2011? Ga dai Isra’ila na yin gaban kan ta har yanzu ta na kai hare-hare cikin Sham kamar yadda ta saba.

Yanzu ta na nuna harin kan makaman tsohon shugaba Assad ne. Idan na Assad ne ai yanzu ga sabuwar gwamnati kuma duk kayan yaƙi ya dace a bar ma ta kayan ta. Idan wani ya yi tunanin Isra’ila na mara baya ga mayakan nan to lokaci ne zai nuna don ga ɗabi’ar Isra’ila ba ta da abokiyar hulɗa sai wacce ta miƙa wuya da yarda da duk muradun Isra’ila da zaman ta daram a yankunan Falasɗinawa ba tare da sukar ta ba. Shin mayakan nan za su cigaba da zuba ido Isra’ila na cin Karen ta ba babbaka a cikin ƙasar su? Amsa a nan zai yi wuya don mayaƙan na aiyana kan su a matsayin masu Jihadi ne don ɗaukaka kalmar Allah. Don haka za su tamkawa Isra’ila kuma daga hakan ya faru wata sabuwar fitina ka iya ɓarkewa shikenan sai a nemi maida Sham ƙasar da ba gwamnatin tsakiya mai ƙarfi. Ga misalin Somaliya da har yau ta ke cikin rikici da ya sa ba mai sha’awar ya wanke kafar sa ya ce zai ziyarci birnin Mogadishu. Kasa na samun ƙarfi ne da yanda shugabanni ke da karɓuwa da kuma huldar arziki da makwabta da sauran manyan ƙasashen duniya.

Isra’ila ta ƙara kai wani hari ƙasar Sham da ya auna wata ma’adanar makamai a daf da birnin kasuwanci na Adra da ke wajen babban birnin ƙasar Damaskas.

Wannan ma’adanar dai ta dakarun hamɓarerren shugaban ƙasar ne Bashar Al’Asad.

Mummunan harin ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 11 kuma fararen hula.

Isra’ila na ikirarin ta na auna sassa ne na magoya bayan Iran don kawar da barazana daga mayaƙan da ke adawa da ita.

Gwamnatin mayakan Jihadi na Sham ta buƙaci Isra’ila da ta dakatar da waɗannan hare-hare na samaniya.

Malamai daga mayaƙan Hayat Tahrir Al-Sham da su ka amshi ragamar mulkin Sham na huɗubar nuna godiya ga Allah na ƙubutar da ƙasar daga hannun hambarerren shugaba Bashar Al’Asad.

Tsohon shugaban dai bai sake wata magana ba tun nuna tamkar a natse ya bar ƙasar har ranar da mayakan su ka shiga Damaskas inda a halin yanzu ya ke samun mafaka a Rasha.

Malaman na caccakar ƙasar Iran da kuma ƙungiyar mayaƙan Hezbollah da su ka riƙa ambata da Hezbush Shaidan a hubuar Juma’a.

Kazalika sun gudanar da sallar jana’izar GAIB ga marigaya daga mayaƙan da su ka yi shahada a gwagwarmayar amsar madafun ikon ƙasar.

Malaman na nuna yanzu dai Sham ta dawo hannun asalin jama’ar ta inda ta kuɓuta daga hannun ‘yan Shi’a.

Sabon shugaban hukumar bayanan sirri na ƙasar Sham/Siriya Anas khaddab ya ce za su yi garambawul ga hukumar.

Khaddab na magana ne bayan nada shi kan wannan mukami da sabuwar gwamnatin ƙasar ta mayaƙan Hayat Tahrir Sham ta yi.

Yanzu dai kusan duk lamuran ƙasar na hannun mayaƙan da ke ƙoƙarin kawo sauye-sauye don bambanta tsarin da na zamanin Assad.

Wannan hukuma na daga cikin waɗanda a ke jin tsaoro a zamanin gwamnatin Assad da a ka kawar.

An buɗe gidajen yarin Sham inda aka sake dukkan waɗanda gwamnatin Assad ke tsare da su.

Mutane sun garzaya gidajen yari don fatar samun ‘yan uwan su a raye da a ka tsare a lokacin yakin basasar ƙasar na shekaru 13 da ya yi sanadiyyar mutuwar kimanain mutum 500, 000.

A gefe ga fitinar Gaza wacce ita ta karya lagon Assad ya rasa tallafi, wani harin samaniya da Isra’ila ta kai kan asibit a arewacin Gaza ya yi sanadiyyar kashe ma’aikatan asibitin 5.

Shugaban asibitin Hossam Abu Safiya ya tabbatar da mutuwar ma’aikatan a mummunan harin da Isra’ila ta kai cikin kuma samamen da ta taƙarƙare a yankin tun watan Oktoba.

Asibitin na Kamal Adwan a Beit Lahia shi ne kaɗai ya saura a yankin da ke kula da majinyata.

Isra’ila dai ba ta yi magana kan harin ba sai dai dama ta ce ta na kai hare-haren ne don hana Hamas sake hada mayaƙa a yankin.

A can Khan Younis kuma da ke kudancin Gaza, yara uku sun rasu a sanadiyyar sanyin hunturu da ya sauka a yankin.

Likitan yara a asibitin Nasser a khan Younis ɗin Ahmad Al-Farra ya ce cikin yaran, ta ƙarshe da ta mutu an kawo ta ne dakin gaggawa don yadda sanyi ya kama ta.

ƙungiyar Hamas ta zargi Isra’ila da kawo wasu sharuɗa da ke tarnaƙi da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Isra’ila dai na son bin dabaru ne na kaucewa janye sojoji a Gaza amma ta na son karɓo mutanen ta da Hamas ke garkuwa da su tun 7 ga Okobar bara.

A ’yan kwanakin nan an koma zama a Doha babban birnin Katar don neman tsagaita wuta da Masar da Katar din har da haɗin kan Amurka ke jagoranta.

Hamas ta fidda sanarwar da ke tabbatar da an dawo yarjejeniya haiƙan amma Isra’ila na kawo sharuɗa kan janye sojojin ta daga Gaza da har kullum ke kawo cikas ga tsagaita wuta.

Fiye da Falasɗinawa 40,000 Isra’ila ta hallaka a Gaza a fiye da shekara daya na wannan yaƙi kuma akasarin waɗanda su ka mutu mata ne da ƙananan yara.

Firaministan katar Sheikh Muhammad bin Abdulrahman bin Jassim Althani ya gana da tawagar Hamas a birnin Doha don ƙarfafa tattaunawar tsagaita wuta na yaƙin Gaza.

Tawagar Hamas na bisa jagorancin babban jami’in ƙungiyar gwagwarmayar Khalil Alhayya.

Ba sabam ba ga Firaministan shiga kai tsaye tattaunawar sulhun amma ya gana da tawagar ta Hamas inda a ka yi bitar hanyoyin neman dakatar da yaƙin Gaza da shafe fiye da shekara ɗaya Isra’ila na ruwan boma-bomai.

ƙatar, Masar da haɗin kan Amurka ke shiga tsakanin don tabbatar da yarjejeniyar amma sai kamar an yi nasara sai a samu cikas kan wasu sharuɗɗa musamman daga gefen Isra’ila.

Althani ya nuna kwarin guiwar za a samu nasarar ƙulla sabuwar yarjejeniyar don nasarar Donald Trump a zaɓen dawowa fadar White House.

Kammalawa;

Me zai sauya yayin da zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump ke shirin karɓar madafun ikon fadar White House? Babbar magana na kan manyan ƙasashen Larabawa irin Daular Larabawa, ƙatar, Masar, Saudiyya har ma da Jodan wajen aiki tare don samun zaman lafiya a Gaza da Sham.