Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Ranar 5 ga watan nan na Nuwmba 2024 za a gudanar da sabon zagayen zaɓen shugaban ƙasa a Amurka. Dama irin tsarin zaɓen Amurka daidai ya ke da irin na Nijeriya wato ya kan zo bayan shekaru 4 kuma ya fi zafi tsakanin ‘yan takara biyu na mafi tasirin jam’iyyu. Bambancin ya na ga yadda jam’iyyu biyun a Amurka ke iya samun damar hawa karaga a tazarar shekaru 4 ko 8 ba kamar Nijeriya inda jam’iyya ɗaya ke tsayin dakar zama kan kujera har abada ba. Amurka na da tasiri a jujjuya siyasar duniya don haka zaɓen ta kan zama abun zuba ido da fata ga dan takarar da a ke ganin zai kamanta adalci ba ga cikin gida kaɗai ba har da sauran sassan duniya. A matsayin Amurka na mai kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar ɗinkin Duniya ta kan zama cikin ƙasashe da a ke fatar adalcin dimokraɗiyyar gwamnatin ta don ɗaukar matsayar da ta dace ga hawa ko ƙin hawa kujerar na ki. Babban abun da ya fi damun akasarin ƙasashen duniya shi ne tsaro ko yadda yaƙe-yaƙe kan hargitsa duniya. Amurka na da tasiri ainun a kusan duk wani yaƙi da ke faruwa ko da ya taɓa faruwa a duniya tun yaƙin duniya na farko zuwa yaƙin cacar baki bayan yaƙin duniya na biyu da ya fi shahara tsakanin Amurka da tsohuwar tarayyar Sobiyet.
A zahiri manyan ƙasashe masu ƙarfin faɗa a ji a duniya ba sa yaƙi da juna kai tsaye sai dai a kaikaice ta hanyar taɓa muradun juna. Misali ƙarara shi ne yaƙin basasa da a ka yi a ƙasar Sham wato Siriya an ga yadda Amurka da Rasha ke marawa ɓangare daban da na juna baya. Ma’ana yayin da Amurka ke tallafawa ‘yan gwagwarmaya ita kuma Rasha na kare gwamnatin ƙasar ne ta Bashar Al’Asad. Mu duba yaƙin Yukrain da Rasha ke ɗamarar hana ƙasar shiga ƙungiyar tsaron ƙasashen yamma NATO kun ga a nan Amurka ba ta ƙaddamar da yaƙi kai tsaye kan Rasha ba amma ta ɗau matakan ƙarfafa damarar yaƙin shugaban Yukrain ne ɓladimir Zelenskyy. Hakanan yadda Amurka ke nuna ƙin jinin mulkin soja a nan Afurka ta yamma ya sha bamban da muradun Rasha. Hakan ya sa ƙasashe da su ka haɗa da jamhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso da su ka tsunduma mulkin soja ke ƙarfafa dangantakar su da Rasha. A kan Iran ma a na ganin yadda ƙasar ke ɗanyen ganye da Rasha a siyasar duniya fiye da Amurka da ta sanya takunkumi kan ƙasar. Haƙikaƙa duniya kusan ta rabu gida biyu tsakanin mabiya Amurka da kuma mabiya Rasha. Wataƙila wani zai yi tunanin Faransa da Sin ta wajen tasiri da su ke da shi. Waɗannan ƙasashen na da irin muradun da su ke karewa a ƙasashen duniya da ba irin na ƙarfin Amurka da Rasha ba. Gwamnatocin duniya kan yi takatsantsan wajen fito na fito da waɗannan manyan ƙasashen biyu amma kan Amurka ya fi tsanani don ba ta shayin kashe kuɗin ta da tura dakarun ta wata klƙasa don kare hulɗar da ta ke da shi ga wannan ɓangare ko wancan. Ai ma sanennen abu ne ko da a kafafen labaru yadda a ke zayyana Amurka a matsayin ‘yar sandar duniya. Amurka ta samu wannan kambun ga yanda ta ke hawa ko tasiri a yanke hukunci musamman a kwamitin tsaro na majalisar ɗinkin duniya.
Amurka na da sansanonin soja a kusan dukkan sassan duniya da hakan ke sa cikin sauƙi ta ke ɗaukar mataki don kare muradun ta da na ƙawayen ta ta fuskar ƙarfin soja. Hatta yanda Amurka ta janye bayan shekaru kimanin 20 daga Afghanistan, ba ya nuna ba ta cimma muradun ta ba ne a ƙasar, a’a ya kai ga lokacin da ba ta da wata riba ko wata manufar da ta ke son cimmawa a ƙasar. Ga Iraki da Amurka ta jagoranci kawar da tsohon shugaba Saddam Hussaini, kusan muradin Amurka shi ne na kawar da tsohon shugaba bayan bayanin ya na mallakar makamai na kare dangi duk da bayanai daga bisani sun nuna ba makaman. Tun kawar da Saddam ma’abota mulkin Iraki su ke ta gwagwarmayar ƙasar ta dawo yanda ta ke amma har yanzu abun bai samu nasara ba. A taƙaice ma Iraki ba ta da wani tasiri a siyasar duniya. Mu duba yanda yaƙin Gaza ke cigaba da gudana fiye da shekara ɗaya kenan kuma a ka kasa tsayar da yaƙin duk da kiraye-kiraye daga ƙasashen duniya da dama har ma da hukuncin kotun duniya a birnin Hague, amma a na da yaƙinin inda Amurka na da muradin yaƙin ya tsaya cak da kuwa ya tsaya. Mun tuna yadda kusan sau 4 Amurka na hawa kujerar na ƙi a kwamitin sulhun majalisar ɗinkin duniya kan wa imma ayyana yaƙin da Isra’ila ke yi kan Gaza na ƙare dangi ne ko kuma a ma dakatar da yaƙin. Amurka kan bugi ƙirji ta dau matakin kare muradun ta ko da kuwa ita kaɗai ce ke da irin muradin. Wato gaskiyar magana Amurka kan iya gaban kan ta a muradun ta a duniya fiye da sauran takwarorin ta masu salo na bin ƙarƙashin ƙasa. Tsohon shugaban Amurka Geroge Walker Bush ya taba faɗa a lokacin wani yaƙi na gabar ta tsakiya cewa ko dai ƙasashe ko kasa ta na tare da Amurka ko kuwa ta na tare da abokai ko abokiyar gaban Amurka.
Shirin zaɓen Amurka tsakanin Harris da Trump
Tsohon shugaban Amurka Doald Trump ya aza alhakin yaklƙe-yaƙe a wasu sassan duniya da rashin tsarin shugaban Amurka Joe Biden.
Trump wanda shi ne dan takarar jam’iyyar Rifabulikan a zaɓen Amurka da a ke shirin gudanarwa a Nuwambar nan, na magana ne kan yaƙin Gaza da kuma Yukrain.
Donald Trump ya ce in da shi ne a kujerar mulkin White House da ma ba a kai harin 7 ga Oktobar bara a cikin Isra’ila da ya kawo yaƙin da a ke yi na Gaza ba.
Trump na zantawa da wakiliyar kafar labaru ta Al-Arabiya inda ya ce da duk ba a yi asarar rayukan da a ka yi ba.
Tsohon shugaban ya ce ya na da muradin dawo da yarjwjeniyar dangantakar tarihi ta Larabawa da Yahudawa wato “ABRAHAM ACCORD” don matso da sassan biyu su riƙa hulɗar diflomasiyya.
A 2020 Trump ya jagoranci ƙulla dangantakar tsakanin ƙasar Bahrain da Daular Larabawa tare da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a fadar White House.
Masana kimiyyar siyasa da wasu masu sharhi na sun fara magana kan zaɓen shugaban Amurka da ke tinkarowa.
Zaɓen na ƙara ɗaukar hankali ne don yadda ta mace ta sake samun damar takara a inuwar jam’iyyar dimokurats wato mataimakiyar shugaba Kamala Harris inda shi kuma tsohon shugaba Donald Trump da ya yi ta tsallake siradin shari’a ya sake samun damar takara a jam’iyyar Rifabulikan.
Masanin kimiyyar siyasa kuma malami a jami’ar Bayero ta Kano Dr.Sa’idu Ahmed Dukawa ya ce kowanne daga ‘yan takarar biyu na da tagomashin lashe zaɓen.
A zantawa ta musamman da Muryar Amurka Dr.Dukawa ya ce in an duba dukkan ɓangarorin biyu na da nau’in masu mara mu su baya kuma ba za a gane maci tuwo ba sai miya ta kare.
Malamin kimiyyar siyasar ya ƙara da cewa Kamala na iya cin gajiyar kasancewar ta mace kuma da samun goyon bayan fitattun tsoffin shugabannin ƙasar, yayin da shi kuma Trump dama yake ware wajen jan hankalin Amurkawa cewa su ne zaɓin sa na farko kuma ba ya sha’awar faɗaɗa lamuran yaƙi a duniya.
Dukawa ya ƙara da cewa farar dabara ce yadda Harris ba ta yage ko nesanta kan ta daga shugaba Joe Biden ba don hakan ka iya sa ta yi asarar goyon bayan sa da kuma wasu jiga-jigan siyasar Amurka irin tsohon shugaba Obama da Bill Clinton.
Kazalika shi kuma Trump ya kan iya fidda kan sa ta hanyar kalamai da kan zuga masu zaɓe su ga shi ne mafita ga Amurka.
Ita kuma mai sharhi kan lamuran siyasa tsohuwar ‘yar siyasa a Nijeriya Mariya Ibrahim Baba ta ce ba za ta yi mamaki ba in Kamala Harris ta lashe zaɓen.
A ra’ayin Mariya Baba, mata na da dabara ta kyauta daga Allah ta hanyoyin jagorantar jama’a.
Mariya Baba da ke marawa siyasar mata baya, ta nuna kwarin gwiwa kan Harris za ta samu nasara duk da Allah shi ke da ikon ba da mulki.
Kammalawa;
Aski dai ya zo gaban goshi. Za a fafata tsaknin Kamala Harris ta jam’iyyar Dimokrats da ke kan mulki da kuma tsohon shugaban Amurka Donald Trump a jam’iyyar Rifabulikan. Koma dai wa ya lashe zaɓen, za mu lura akwai wasu muradun Amurka da ba sa canjawa da ke kare muradin ƙasar ko kambun ta a tasirin tsaro da diflomasiyyar duniya. Duk kalaman ‘yan takarar biyu na zayyana Amurka da cewa ƙasa ce ta musamman mai tasiri. A zahiri bambancin kawai da a ke gani tsakanin ‘yar Dimokurats da Rifabulikan shi marawa baya ga yake-yake a wasu ƙasashe musamman isra’ila da Falasdinawa ta bangaren Dimokrats da kuma muradin kaucewa yaki don tsumulmular kuɗi daga Rifabulikan. Kai hakan ma ba muradun jam’iyyun ba ne a tarihi, muradu ko salon ‘yan takara ne wato a yanzu za a ce yanda shugaba Joe Biden ke tafiyar da lamarin Gaza da yadda Trump ya nemi jawo Larabawa su hada kai da Isra’ila a 2020. In bambancin jam’iyya ne wa ya jagoranci yaƙin tekun Fasha na farko da na biyu? Amsa tsohon shugaban Amurka George H.W Bush da dan sa tsohon shugaban Amurka George Walker Bush duk ‘yan jam’iyyar Rifabulikan!.