Shirin ƙidaya na fuskantar haɗarin ɗagewa saboda rashin kuɗi

Yayin da ya rage ‘yan kwanaki kafin shirin ƙidayar al’umma na ƙasa ya kankama, da alama shirin na fuskantar haɗarin ɗagewa saboda ƙalubalen kuɗi da sauran kayan aikin da yake fuskanta.

Bayanan da Manhaja ta tattaro na nuni da cewar, akwai yiwuwar Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa ta ɗage shirin saboda rashin kuɗi.

A farkon watan Maris, yayin wani taro a Abuja, an jiyo Ƙaramin Ministan Kasafi da Tsare-tsare, Clem Agba, ya ce Gwamnatin Tarayya ta shirya samar da ƙoƙon bara domin tara kuɗin da za ta yi amfani da shi wajen gudanar da shirin ƙidaya na 2023.

Agba ya ce Naira biliyan
869 Hukumar ke buƙata don gudanar da shirin.

Ya ƙara da cewa, Gwamnati ta riga ta miƙa biliyan N291.5, amma kuma akwai buƙatar ƙarin biliyan N327.2.

A cewar Agba, tun bara ya kamata a gudanar da shirin amma aka ɗage shi zuwa Maris, 2023, inda aka ba da shawarar a sake ɗage shirin zuwa watan Mayu.

Ya ce, “A shekarar 2006 aka gudanar da shirin ƙidaya na ƙarshe a Nijeriya. Sannan a 2014 gwamnatin baya ta nuna buƙatar sake gudanar da shirin a 2016 daidai da shawarar Majalisar Ɗinkin Duniya.

“Sai dai har wa’adin gwamnatin ya ƙare a 2015 ba tare da cika ƙudurin ba. Daga 2015 zuwa 2016, ƙasar ta yi fama da koma bayan tattalin arziki sakamakon faɗuwar farashin mai da koma baya a samar da man.”

Haka dai al’amari ya ci gaba da wakana har zuwa lokacin da aka gudanar da babban zaɓen 2023, wanda hakan ya sake sa aka ɗage shirin ƙidayar zuwa 3-5 ga Mayu, 2023, wanda hakan ke nufin sau biyu ana ɗage shirin ƙidayar.