Shirin ceto ɗaliban Kebbi: Mafarauta sun ja da baya saboda rashin cika alƙawarin gwamnati

Mafarautan jihar Kebbi da suke ba da gudunmawarsu wajen ƙoƙarin ceto ɗalibai sama da ɗari da ma’aikatan da aka yi garkuwa da su daga Sakandaren Tarayyar da ke Yauri, sun bayyana cewa sun dawo daga rakiyar yunƙurin ceto ɗailabn da aka yi a jihar.

Mafarautan sun ce sun ɗauki wannan mataki ne saboda kulawar da ba su samu ba daga ɓangaren gwamnatin jihar.

Kafin wannan lokaci, sojoji sun bayyana nasarar da suka samu wajen kuɓutar da ƙalilan daga ɗaliban haɗa da ma’aikaci guda, tare da cewa wasu daga cikin ɗaliban sun rasu, yayin da su ma ‘yan sandan jihar Zamfara suka ba da sanarwar ceto ƙarin ɗalibai biyu.

Sama da kwanaki 45 ke nan da yin garkuwa da waɗanda lamarin ya shafa ba tare da wani ƙwaƙƙwaran yunƙuri daga ɓangaren gwamnatin Kebbi da hukumomin tsaro wajen ganin an ceto ɗaliban ba.

A can baya, an ruwaito Gwamnan Kebbi, Abubakar Bagudu, ya sha alwashin shige wa mafarauta da ‘yan bijilanti na jihar gaba wajen gwagwarmayar ceto ɗaliban.

Da yake zantawa da jaridar Premium Times a ranar Laraba, ɗaya daga cikin shugabannin mafarautan jihar Kebbi, Abdu Bagobiri, ya ce sun janye daga aikin ceto ɗaliban saboda a cewarsa, gwamnatin jihar ta nuna rashin gaskiya wajen ƙin cika alƙawuran da ta yi musu.

A cewar Bagori: “Ba haka kawai muka soma wannan aiki ba face da sanin gwamna, kuma ya yi mana alƙawarin zai tallafa mana da kuɗaɗe sai dai ba mu ga ƙoƙarinsa kan hakan ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *