Shirin horar da matasa na Muntari Ishaƙ ƙalubale ne gare ni – Doguwa

Dag MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Dan Majalisa mai wakiltar ƙaramar Hukumar Doguwa da Tudun Wada a Majalissar wakilai ta Tarayya da ke Abuja, Hon Alasan Ado Doguwa, ya bayyana cewa yadda tsohon Shugaban ƙaramar Hukumar Birnin Kano, kuma tsohon kwamishinan komai da ruwanka a Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje Hon. Muntari Ishaƙ Yakasai ke yi na ɗaukar nauyin horar da matasa sana’o’i da ɗaukar nauyin su, su yi ilimi daga ƙananan hukumomi 44 a wannan cibiya da ake kira ɓIT, da Hon Muntari ke shugabantar ta da ɗaukar nauyin matasan da suke samun horo tun 2018 zuwa yau, “wannan babban ƙalubale ne gare ni ga kuma ɗaukacin dukkan wani mai muƙamin gwamnati a kowacce jam’iyya, ya ke kuma ƙalubale ne ga dukkan wani mai hali da ke da kishin al’umma da Kano da ma Nijeriya bakiɗaya domin ta haka ne za a samu matasa masu aikin yi da zai kawar da abubuwa marasa kyau da matasa ke yi kuma a samu cigaban tsaro, wannan  abin a yaba wa Hon. Muntari Ishaƙ Yakasai ne,” kamar dai yadda Hon. Alhassan Ado Doguwa bulaliyar majalissar wakilai ta Abuja a lokacin da ya ke gabatar da jawabi a matsayin san a babban baƙo, a wajen taron yaye ɗalibai 1410 da Muntari Ishaƙ ya ɗau nauyin karatunsu da koyar da su sana’o’ in zamani domin dogaro da kansu wanda aka gabatar a ƙarshen makon da ya gabata.

Shi ma a jawabinsa Hon. Muntari Ishaƙ bayyana farin cikinsa ya yi kan damar da Allah ɗadaukakin sarki ya bashi na yin wannan aiki na alkairi ta yadda dubban matasa aka koya musu sana’o’i irin ilimin komfuyota ɗaukar hoto mai motsi da marar motsi har ma da koyar da aikin Jarida da sauran sana o i na zamani na maza da na mata, a wannan cibiya wanda yanzu haka wasu da dama  suna aiki a kafofin yaɗa labarai da sauran kanfanoni na gwamnati da masu zaman kansu sakamakon horan da suka samu awannan cibiya ta ɓIT.

Haka kuma Hon Ishaƙ ya sha alwashin cigaba da yin wannan aiki na horar da matasa sana o i da basu tarbiyar aiki da kyakkawar mu,amala da abokanan mu,amalarsu ta aiki ko ta ciniki da sauran mu,amalar yau da kullum kuma na ya bawa ɗaukacin mahallata wannan taro tun daga kan Hon Alhassan Ado Doguwa da irin gudunmawarsa da su Majidaɗin ƙiru tsohon kwamishinan ilimin Jihar kano da sauran jagororinmu na jam’iyyar APC kamar shugaban jamiya na ƙasa Dr Abdullahi Umar Ganduje da sauran yan uwa da masoya kan irin gudunmawa da goyan bayan, haɗin kai da muke samu a dukkan al’amuran cigaban al’ummar Kano da Nijeriya.