Shirin kai hari: Yadda `yan bindiga suka gargarɗi sojoji da su bar ƙauyen Miango

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsagerun ‘yan bindiga sun shaida wa Sojojin Nijeriya da ke aikin samar da tsaro a ƙauyen Miango da ke cikin Ƙaramar Hukumar Bassa, Jihar Filato, cewa su bar yankin domin za su sake kai wani hari kan ‘yan ƙauyen.

Kwanan nan ne dai aka girke sojoji yankin bayan rahoton wani hari da ‘yan bindiga suka kai a kauyen na Miango.

Rundunar soji wadda ke aiki ƙarƙashin Rundunar Safe Haven, a watanni biyu da suka gabata ta ce ta yi ƙoƙarin dakatar da maharan ga afka wa ‘yan ƙauyen.

Wasu shaidun gani da ido waɗanda ba sa son a bayyana sunansu, sun shaida wa jaridar TheCable cewa, maharan sun rubuto wa jama’ar ƙauyen wata wasiqa ne cewar su sanar da rundunar sojin da aka jibge su bar yankin, domin za su kawo wa ‘yan ƙauyen wani hari.

“Mun riga mun saka jami’an mu ta iyakar ƙauyen da kuma tsaunukan da waɗannan mahara suke fitiwa,” a cewar wata majiya.

“Sau da dama sukan yi ƙoƙarin tsallakowa cikin ƙauyen, amma rundunar mu tana dakatar da su da ɓarin wuta. Wata guda da ya wuce ma, mun yi ba-ta-kashi da su, inda har muka rasa sojojin mu biyu.

“Haka ma kwanan nan ‘yan ƙauyen sun kawo mana wata wasiƙa da take nuna cewa daga maharan take, inda suke sanar da sojoji cewa su bar yankin don za su kawo hari. Haka kuma maharan sun yi barazanar idan sojojin ba su bar yankin ba, to su ne na farkon waɗanda za su kai wa harin.”

Sai dai wata majiya mai alaka da Rundunar Soji ta ce tuni aka sanar da hedikwatar tsaro domin ɗaukar matakin gagggawa.

Wasu kwamandojin soji a yankin sun bayyana cewa kwanan nan sun yi yunƙurin samar da zaman lafiya tsakanin maharan da kuma ‘yan ƙauyen, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

Wata majiya ta shaida cewa an gayyaci ɗaya daga cikin kwamdojin ‘yan bindigan domin yin sulhu a tsakani, bayan da aka kashe wasu manoma a gonakin su.

“Saboda ba su iya shiga ƙauyen su kai hari, domin sojoji za su dakatar da su, yanzu kawai suna jira ne manoma su je gonakin su, daga can sai su far mu su,” kamar yadda majiyar ta bayyana.

“Abu ne mawuyaci a ce duk wanda zai je gonarsa a ƙauyen sai sojoji sun raka shi, saboda haka muka ce za mu samar da zaman lafiya ta hanyar yin sulhu da mutanen nan.

“Har mun riga mun yi yarjejeniya a tsakani cewa ba za su sake kai wa ‘yan ƙauyen hari ba. Aƙalla zuwa yanzu an shafe kusan sati uku babu wani manomi da aka kashe ko aka yi garkuwa da shi.

“Mun girgiza ƙwarai da gaske da ganin barazanar da suka yi, amma rundunar mu tana a shirye, kuma ba za mu bari su karɓe wannan ƙauye ko su ci galaba a kan su ba,” a cewar majiyar.