Shirin KEEP na Gwamna Bala ya ƙarfafa tattalin arzikin mutane 8,000

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Shirin ƙarfafa Tattalin Arzikin Jama’a na Ƙauran Bauchi, kuma Gwamnan jiha, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed wanda aka yi wa laƙabi da ‘Ƙaura Economic Empowerment Programme (KEEP) da aka ƙaddamar a bara, a yanzu haka ya rarraba kuɗaɗe da kayayyakin sana’o’i daban-daban waɗanda a jimlace sun tasar ma Naira biliyan guda da miliyan dubu ɗari biyu kyauta wa mutane dubu takwas da ke cikin ƙananan hukumomi goma sha shida na jihar.

Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya ce har-ila yau gwamnatinsa ta rarraba KeKe Napep guda 1,000 ga ‘yan acaɓa da motoci bus-bus guda 154 lokacin da aka ƙaddamar da shirin na KEEP, akan bashi maras ruwa, waɗanda za a riƙa biyan bashin wata-wata, tare da juya kuɗaɗen ana sayo wasu motocin da zummar waɗansu mutane ma su amfana.

Da yake ƙaddamar da shirin a ƙananan hukumomin Ningi da Warji, waɗanda sune na 15 da 16 da ake ƙaddamar wa tunda aka fara, gwamnan ya bayyana cewar, a kowace ƙaramar hukuma, gwamnati tana raba tsakanin kuɗaɗe da kayayyakin sana’o’i na jimlar Naira miliyan saba’in da biyar kyauta domin jama’a su ƙarfafa tattalin arzikinsu, yana mai bayyana cewar, yanzu ƙananan hukumomin Bauchi, Katagum, Alkaleri da Kirfi ne suka rage wajen cin gajiyar wannan shiri na gidauniyar Ƙauran Bauchi.

Gwamna Bala ya bayyana cewar, a ƙarƙashin wannan tsari, a cikin kowace ƙaramar hukuma na ƙananan hukumomi goma sha shida da aka ƙaddamar da shirin, akan raba kayayyakin sana’o’i daban-daban, da kuma kuɗaɗe waɗanda a jimlace sun kai Naira miliyan saba’in da biyar wa zaɓaɓɓu waɗanda suka ci gajiyar shirin.

Kowane mutum daga cikin zaɓaɓɓun maciya gajiyar wannan shiri guda ɗari biyar a kowace ƙaramar hukuma a kan bashi/bata kayan yin sana’a da tsabar kuɗi Naira dubu hamsin domin bunƙasa jarin sa/ta, da samar da babur na hawa guda uku a kowace mazaɓa dake cikin ƙananan hukumomi guda ashirin na jihar, waɗanda za a raba wa kowane shugaban PDP, kodinata da shugaban matasa a kowace mazaɓa a matsayin masu cin gajiyar shirin.

Sauran, kamar yadda gwamna ya zayyana, sun haɗa da bayar da kuɗaɗe Naira dubu ɗari wa kowane shugaban matasa da shugabar mata a kowace ƙaramar hukuma guda ashirin dake cikin jihar, da kuma bayar da motoci bus-bus guda biyar wa kowace ƙaramar hukuma na ƙananan hukumomi ashirin na jihar.

Ƙauran na Bauchi ya ce gwamnatin jiha a ƙarƙashin jagorancinsa ta bayar da matuƙar fifiko kan ƙarfafa tattalin arzikin jama’a ta hanyar samar sana’o’in yi a cikin yunƙurinta na kawar da talauci a tsakanin jama’a, don haka ta samar da cibiyar hada-hadar kuɗaɗe da zai kasance majadala wa shirin KEEP ta yadda zai kasance kadarko wa cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe, kana ya ƙulla dangantaka a tsakanin cibiyoyin da wasu cibiyoyin hada-hada ta yadda zai wanzar da hada-hadar kuɗaɗe mai ɗorewa a cikin tsarin.

“Shirin ɗungurugum ɗinsa yana da zummar mayar da jama’ar jihar Bauchi masu dogaro da ƙafafunsu ta hanyar samar masu madafun dogaro da kyakkyawan yanayi na bunƙasa tattalin arziki, domin an zayyana shine ya bunƙasa hada-hadar kuɗaɗe ta yadda zai shawo kan matsalolin rashin ayyukan yi da kawar da talauci a tsakanin al’umma, musamman mata da matasa majiya ƙarfi.”

Gundarin manufar, inji gwamna, ita ce ta sauƙaƙa wa talaka shiga cikin hidimomin kuɗaɗe ta yadda zai bunƙasa sana’ar sa da zamantake wa cikin kasuwanci, tare da kawar da talauci, yayin da shirin KEEP yake da manufar ƙarfafa da goyawa jama’a baya su tsumduna cikin haƙƙoƙin kasuwanci.

Gwamna Bala sai ya yi kira ga masu cin gajiyar shirin na ƙarfafa tattalin arziki da su alkinta kuɗaɗe da kayayyakin sana’o’i da aka samar masu kyauta domin inganta arzikinsu, tare da taimaka wa waɗansu da za su gwamatse su, yana mai bayar da tabbacin gwamnatin jiha za ta cigaba da zaƙulo hanyoyi daban-daban na kawar da talauci a tsakanin jama’ar ta.

Sanata Bala Mohammed ya kuma jaddada wa jama’ar jiha cewar, gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba bisa aniyar ta na bunƙasa tattalin arzikin jama’a duk da ƙarancin kuɗaɗe da take shiga cikin lalitarta.