Shirin kula da ilimin yara milyan 6.9 ya kankama – inji Gwamnatin Tarayya

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa, ta soma gudanar da shirinta na neman bai wa yaran da suka daina zuwa makaranta ilimi a faɗin ƙasa.

Sanarwar hakan ta bayyana ne a shafin tuwita na Shugaban Ƙasa a Larabar da ta gabata.

Idan dai za a iya tunawa, a Janairun da ya gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa wani kwamiti na musamman mai mambobi 18 tare da ɗora masa nauyin kula da wannan shiri, ƙarƙashin jagorancin Ministar Jinƙai da Agaji da kuma Ministan Ilimi.

Buhari ya ce, shirin zai maida hankali ne wajen karantar da yara darussan Lissafi da Harshen Turanci da Ilimin Zamantakewa da kuma Darasin Kimiyya.

Ya ce, “Mun soma gudanar da shirin musamman don kula da karatun yaran da suka daina zuwa makaranta a faɗin ƙasa.

“Za mu tabbatar da cewa shirin bai baro yaro ko guda a baya ba.”