Shirin miƙa mulki: Buhari da gwamnoni za su sake bayyana kadarorinsu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo da ministoci 44 a Majalisar Zartarwa ta Tarayya da gwamnoni 28, za su ƙara bayyana kadarorinsu kafin ranar 29 ga watan Mayu da wa’adinsu zai kare.

Bayyana kadarori ga dukkanin masu muƙaman gwamnati wajibi ne, kuma Hukumar Ɗa’ar Ma’aikata ta ce a shirye ta ke za ta fara ba su fom domin su bayyana kadarorinsu kafin ranar 29 ga watan Mayu na wannan shekara da wa’adin su zai ƙare.

Waxanda za su karvi wannan fom ɗin su ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da gwamnoni 28 da ministoci 44 da hadiman su, ‘yan majalisar dokokin ƙasa da na jihohi, da shugabanin ƙananan hukumomi kamar yadda aka tsara a kundin tsarin mulkin ƙasar.

Masana sun ce a ƙarƙashin sashe na 172 zuwa 209 na kundin tsarin mulki Nijeriya ya zama dole ga dukkan ma’aikaci ko da ƙaramin ma’aikaci ne ko kuma babban ma’aikaci, matuƙar dai kana karɓar kuɗi daga baitulmalin gwamnati, to ya zama tilas mutum ya bi wannan umarnin.

Masana sun ce ganin cewa ana iya take dokar ya sa aka kafa kotun hukunta ma’aikata, wacce aka fi sani da CCB ko kuma Code of Conduct Bureau a turanci.

Mainasara ya qara da cewa anan ne ake hukunta duk wanda aka same shi da laifin saɓa wa dokokin aiki wanda hukumar ɗa’ar ma’aikata ke sa ido akai idan mutum ya saɓa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *