Shugaba Buhari ya ba mu ƙarfin gwiwar kafa masana’antar cashe shinkafa – Ibrahim Gerawa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Shugaban rukunin kamfanin Gerawa, Alhaji Ibrahim Muhammad ya bayyana godiya ga Allah da ɗimbin jama’ar da suka zo aka buɗe sabon katafaren masana’antar sarrafa shinkafarsu ta Gerawa lafiya.

Ya ce ba domin irin waɗannan kamfanoni da aka samar ba, da yadda aka karbi umurnin shugaban ƙasa na a noman shinkafa ƙasar nan da ba a san yadda za a yi da shinkafar ba. Don maganin hakan, tunda Allah ya hore musu, shi ya sa suka kafa injina na sarrafa kayan gona da manoma ke samar wa don ya kasance an yi noman an sayar da daraja kuma mutane su amfana.

Alhaji Ibrahim Muhammad ya yi kira ga al’ummar ƙasar nan musamman manoma su fito su faɗaɗa gonaki su yi noma, kamfanoni sun fito da yawa irin nasu, suma ga shi suna qara faɗaɗawa, don haka a fito a yi noma in Allah ya yarda da taimakon Allah za a sayar har gona za a bi manoma a rinƙa saya a kawo kamfani a sarrafa.

Gerawa ya yaba wa Maigirma Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da ya ɗauki nauyin taron. Sannan ya kuma gode wa Gwamnan Jigawa Alhaji Abubakar Badaru da shi ne ya gayyato Babban Gwamnan Bankin Nijeriya da sauran gwamnoni.

Shi ma da yake zantawa da ‘yan jarida. Alhaji Abubakar Usman Bello, Manajan Darakta na kamfanin sarrafa shinkafa na Gerawa, ya ce sun gode wa Allah bisa kafa harsashin sabon kamfanin na biyu da buɗe wanda yake aiki yanzu da yake sarrafa ton 400 a rana ɗaya. Wanda saboda za a gama nan gaba, zai bada sama da haka a rana.

Ya ce in aka dubi yadda Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari ya hana shigo da abubuwa da za a iya nomawa a ƙasa ta havaka noma ya ƙarfafa wa manoma gwiwa da bunƙasa kamfanoni wajen samarwa matasa ayyukan yi.

Alhaji Abubakar Usman ya daɗa jan hankalin manoma a arewacin ƙasar nan da cewa duk shinkafar da za su noma yanzu za su saya su sarrafata har daga ƙasashen waje ma suna sayen shinkafa bayan ta gida.

Ya ce a yanzu suna niƙa tan 400 a kullum. Sannan shinkafarsu ta Gerawa tana gogayya da irin wacce ake kawowa daga waje kuma ko’ina daga sassan ƙasar nan ana zuwa sayen shinkafar.

Manajan Darakta na kamfanin sarrafa shinkafar ta Gerawa ya ce saboda jajircewar shugaban kamfanin na Gerawa sai da ya zaga ƙasashen duniya ya samo injina masu nagarta na sarrafa shinkafa da kyau da ake aiki da su. Sannan akwai ɗaruruwan mutane da suke aiki a ɓangarori daban-daban na masana’antar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *