Shugaba Buhari ya kyauta da ya buɗe iyakokin ƙasa, inji Ibrahim Migini

Daga MOHAMMED ALI, a Gombe

An jinjina wa Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari saboda bubbuɗe wasu kan iyakokin ƙasar nan da ya yi kwanan nan.

Alhaji Ibrahim Abdulkadir Migini, Shugaban kamfanin Migini Investment a babbar kasuwar Gombe, shi ne ya yi jinjinar a hira da ya yi da manema labarai a cikin kamfanin sa a Gombe a ƙarshen mako.

Migini ya yi nuni da cewa, bubbuɗe kan iyakokin huɗu da Buhari ya bada umurni a yi, ba ƙaramin alfanu ba ne saboda ‘yan Nijeriya yanzu za su samu mafita daga irin tsadar rayuwar da rufe iyakokin ta haddasa, yana mai bayanin cewa “babu shakka, yanzu al’umma za su fahimci cewa buɗe kan iyakokin alheri ne garesu, saboda jim kaɗan nan gaba kayayyaki za su fara arha a kasuwanni, musamman abinci da kayan masarufai. To kaga ba ƙaramin abin alheri ne Baba Buhari ya yi ba.”

Sai ya shawarci ‘yan Nijeriya da su kiyaye kar su rinƙa shigowa da haramtaccen kayayyaki ta iyakoki kuma jami’an tsaro su tabbata sun sa ido sosai akan duk abin da zai shigo cikin ƙasa ko zai fita.

Alhaji Ibrahim Migini sai ya yi kuka ga Gwamnan Gombe Alh. Muhammadu Inuwa Yahaya da ya rungumi ‘yan kasuwar jihar ta tallafa musu domin su qara faɗaɗa harkokin su, su ƙara ɗaukar matasa aiki su kuma ƙara bunƙasa kuɗin shigar yankin.

Ɗan kasuwan wanda ya ce yana da ma’aikata sama da 100 wasu da yawa masu iyali, sai ya gode wa Allah da kuma gwamna da Mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar, saboda zaman lafiya mai ɗorewa a jihar, saboda a cewar shi, idan ba zaman lafiya ba cigaba ta kowace fannonin rayuwa.

Ya kuma yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya akan aikin da hukumar tsabtace muhalli ta jihar wato (GOSEPA) take yi saboda ƙwarin gwiwwar da gwamna ya yi musu, baya ga kuma gyare-gyaren hanyoyi a faɗin jihar da lantarki lungu da saƙo da ya kai.

Daga ƙarshe, Migini ya yi fatan Musulmi sun yi bukukuwan ƙaramar Sallah lafiya.