Buhari ya rantsar da shugaban hukumar zabe ayau

Ayau ne shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da shugaban hukumar zabe ta kasa, Farfesa Mahmoud Yakubu a karo na biyu. Shugaban ya rantsar da shi ne, kafin fara zaman zauren kwamitin zartarwa na gwamnatin tarayya, bayan an gabatar da jim na minti daya, domin tunawa da marigayi tsohon ministan tsaro, Domkat Bali.

In ba a manta ba, tun ran 27 na watan Oktoba ne, shugaban ya nemi sahelewar majalisar dattawa akan zai mayar da shugaban a karo na biyu. Wannan amincewa da majalisa ta yi, na nufin Farfesa Yakubu ne mutum na farko da ya taba rike hukumar sau biyu.

Farfesa Yakubu dai ya rike mukamai da dama, kafin darewarsa kan karagar shugaban zabe na kasa, in da ya gaji Farfesa Attahiru Jega, tun bayan kammala zaben 2015.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*