Buhari ya yi amai ya lashe

Akwai alamun cewa, shugaba Buhari, ya lashe amansa da ya yi, akan saka rana da zai ziyarci majalisar kasa, domin yi musu bayani akan matsalar tsaro da kuma dalilan da su ka hana shi canja manyan hafsoshin  tsaron kasar nan.

A yanzu haka dai an tabbatar da cewa, tun bayan ganawarsa da gwabnonin Jam’iyyar ta APC ne, shugaban ya canja wannan shawara ta sa.

Wata majiya da muka zan ta da ita, ta bayyana mana cewa, wannan sauyi ya taso ne, bayan Jam’iyyar sun sami labarin cewa, yan majalisar da ke bangaren jamiyyar adawa ta PDP sun yi wa shugaban kwanton bauna, in da suke jiran zuwan nasa, domin su titsiye shi, har sai yayi musu cikakken bayani.

Gwamnonin na Jam’iyyar sun baiwa shugaban shawarar da maganin kar ayi, to kar a fara. zuwan sa gaban majalisar zai bai wa yan adawa damar yi wa shugaban hawan kawara.

Su kansu Sanatocin na APC sun nuna goyon bayansu ga wannan mataki da fadar shugaban ta dauka.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*