Shugaba Ramaphosa ya haramta sayar da giya lokacin Easter a ƙasarsa

Daga WAKILINMU

Shugaban Ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya ɗauki matakin haramta sayar da giya na kwanaki huɗu lokacin bikin Easter domin daƙile yaɗuwar cutar korona, inji RFI.

Da yake jawabi ga al’ummar ƙasarsa, Shugaba Ramaohosa ya ce sun gano cewar mutanen da suka kwankwaɗi giya na aikata laifuffukan da ba su dace ba waɗanda ke yaɗa cutar korona.

Don haka ya ce daga ranar juma’a zuwa Litinin masu zuwa, ba za a sayar wa mutane giyar su kai gida ba. Amma za a bar ta ga masu sha a gidajen abinci da mashaya.

Mutane sama da miliyan ɗaya da rabi suka kamu da cutar korona a ƙasar, inda mutum 52,700 daga ciki sun mutu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *