Shugaba Tinubu ya dawo daga taron ƙasashen Afirka

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya dawo daga taron ƙungiyar ƙasashen Afrika (AU) da ya halarta a ƙasar Kenya.

Bayanai daga birnin tarayya, Abuja, sun ce jirgin da ya dawo da Tinubu da tawagarsa ya sauka Babban Filin Jirgin Saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ne da misalin ƙarfe 4:20 na ranar Litinin.

Manyan jami’an gwamnati ƙarƙashin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ne suka tarbi Tinubu a filin jirgin saman.

Cikin waɗanda suka yi wa Tinubu rakiya har da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila; Gwamnan Imo; Hope Uzodinnma da kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *