Shugaba Tinubu ya naɗa Argungu a matsayin shugaban hukumar PSC

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa tsohon mataimakin sufetan ƴan sanda na ƙasa, Hashimu Argungu a matsayin sabon shugaban hukumar kula da harkokin ƴan sanda ta PSC.

Argungu ya maye gurbin Solomon Arase ne da shugaba Tinubu ya tsige, wanda ke shugabantar hukumar tun watan Janairun 2023, a lokacin gwamnatin tsohon shugaba Muhammadu Buhari.

Sanarwar ta fito ne daga ofishin mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale a ranar Litinin.

Haka nan, sanarwar ta ce Tinubu ya naɗa Chief Onyemuche Nnamani a matsayin sakataren hukumar da kuma Taiwo Lakanu mai ritaya a matsayin mamba.

Ngelale ya ce nan da wani ɗan lokaci za’a naɗa sauran mambobin hukumar bayan tabbatar da su daga majalisar dattijai ta ƙasa.

Sanarwar, ta ƙara da cewa Tinubu ya naɗa Mista Mohammed Sheidu a matsayin babban sakataren ofishin kula kuɗaɗen hukumar yan sanda.

Ajuri ya ƙara da cewa, shugaba Tinubu ya yi hakan ne domin ganin an samu inganci da nagarta wajen gudanar da ayyukan ƴan sanda da ma amfanin ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply