Shugaba Tinubu ya yi naɗe-naɗen farko a bayan shan ratsuwa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi naɗaɗen farko a matsayinsa na Shugaban Ƙasa.

Wannan na zuwa ne a ranar da ya sha rantsuwar kama aiki, wato Litinin 29 ga Mayu, 2023.

Waɗanda ya naɗa sun haɗa da Ambasafa Kunle Adeleke Babban Jami’in Tsare-tsare (SCOP) ga Shugaban Ƙasa, Dele Alake a matsayin Kakakin Shugaban Ƙasa, sannan Olusegun Dada a matsayin Mai Bada Shawara Kan Sha’anin Yaɗa Labarai na Zamani.

Sa’ilin da yake jawabi jim kaɗan bayan shan ratsuwar kama aiki, Tinubu ya yi alƙawarin kafa majalisarsa cikin ‘yan kwanaki ko makonni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *