Shugaba Xi Jinping ya halarci bikin rufe gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing

Daga CRI HAUSA

An yi bikin rufe gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu karo na 24 a Beijing a daren yau Lahadi, inda shugaban ƙasar Sin Xi Jinping da shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na ƙasa da ƙasa Thomas Bach suka halarci bikin.

A jawabin da shugaban kwamitin wasannin Olympic ta ƙasa da ƙasa IOC, Thomas Bach, ya gabatar a bikin rufe gasar, Bach ya bayyana gasar wasannin Olympic ta lokacin hunturu ta Beijing da cewa “ta musamman ne.”

A gun bikin rufe gasar, an kuma damqa tutar Olympic ga magajin garin Milan da na Cortina d’Ampezzo, biranen da za su karɓi baƙuncin gasar Olympic ta lokacin hunturu ta shekarar 2026.

Murtala Zhang/Ahmad Fagam
​​​