Shugaba Xi ya bada umarnin bada fifiko ga ceton rayuka a gundumar lardin da girgizar ƙasa ta aukawa

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya ba da muhimmin umarnin bayar da fifiko ga aikin ceton rayuka, ba tare da yin ƙasa a gwiwa ba, domin rage asarar rayuka, sanadiyyar girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.8 da ta auku a gundumar Luding na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin ƙasar, a yau Litinin.

Hukumomi a yankin sun ce mutane 21 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar iftila’in.

Lardin ta aike da sama da ma’aikatan ceto 600, kuma 300 sun riga sun isa wurin da iftila’in ya auku domin shiga aikin ceto da gyara tituna da tura jirage marasa matuƙa domin tantance asarar da girgizar ta haifar.

Haka kuma ƙarin jami’an ceto na kan hanyarsu ta zuwa wurin.

Mai fassara: Fa’iza Mustapha