Shugaba Xi ya halarci bikin maraba da Yariman Masarautar Saudiyya ya shirya masa

Daga CMG HAUSA

A yau Alhamis 8 ga wata ne yariman masarautar Saudiyya, kuma firaministan kasar Muhammad bin Salman bin Abdel Aziz Al Saud ya shiryawa shugaban kasar Sin Xi Jinping, a madadin sarkin masarautar Salman bin Abdul Aziz Al Saud.

Yarima Muhammad bin Salman bin Abdel Aziz Al Saud, ya karbi bakuncin shugaba Xi Jinping, yayin bikin da ya shirya masa a fadar masarautar dake birnin Riyadh, a wani bangare na ziyarar aiki da shugaba Xi ke yi a masarautar ta Saudiyya.

Rahotanni sun ce, shugaba Xi ya isa fadar masarautar ne da misalin karfe 12:20 na rana, cikin mota ta musamman da rakiyar jami’an tsaron masarautar dake cikin jerin gwanon babura, da tawagar mahaya dawaki.

Yayin bikin na maraba da zuwan sa, Xi Jinping tare da yarima Muhammad bin Salman bin Abdel Aziz Al Saud, sun kalli faretin girmamawa da rukunin jami’an tsaron masanarautar suka gudanar.

Rukunin jami’an tsaron fadar masarautar sun gabatarwa shugaba Xi faretin martabawa, mai kunshe da sarrafa takubba da salo irin na gargajiyar masarautar.

Mai fassara: Saminu Alhassan