Shugaba Xi ya jaddada aniyar ƙasarsa ta buɗe ƙofa mai nagarta

Daga CMG HAUSA

A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada aniyar ƙasar sa ta buɗe kofa mai nagarta, yana mai cewa Sin za ta ci gaba da bude kofa ga duniya baki ɗaya, ba tare da sauya matsaya ba.

Xi ya yi wannan tsokaci ne, yayin da yake jawabi ga taron cika shekaru 70, da kafuwar hukumar yayata hada-hadar cinikayyar ƙasa da ƙasa, da taron kolin ƙasa da ƙasa na ingiza harkokin cinikayya da zuba jari, da ya gudana ta kafar bidiyo.

Fassarwa: Saminu