Shugaban ƙaramar Hukumar Fika ya yaba wa Buni kan ayyukan raya Yobe

Daga GAMBO ISA a Abuja

Shugaban ƙaramar Hukumar Fika a Jihar Yobe, Honorabul Audu Bukar Gadaka ya yaba wa, Gwamna Mai Mala Buni bisa ayyukan raya ƙasa a jihar.

Gadaka ya bayyana haka ne a cikin makon nan yayin wata tattaunawa da wakilinmu a Abuja, inda ya zayyana wasu daga nasarorin da gwamnan ya samu a fannin jin daɗi da walwalar al’umma ta fuskar kayayyakin more rayuwa, noma, ilimi, kiwon lafiya, gina manyan kasuwanni na zamani da sauransu.

Honorabul Audu Bukar Gadaka ya lissafo nasarorin da suka haɗa da, shirye-shiryen da suka shafi al’ummar jihar kaitsaye, kamar gina manyan kasuwannin zamani a ƙananan hukumomi 17 ciki har da Damaturu babban birnin jihar, Nguru, Bade, Potiskum da Gaidam.

Honorabul Audu Bukar Gadaka ya yaba da aikin gine-gine tare da gina babbar kasuwar zamani a gundumomin da ke cikin garin Fika.

Honorabul Audu Bukar Gadaka, ya yaba da yadda gwamnan ke yaƙi da ‘yan ta’adda, inda Gwamna Buni yake taimaka wa  jami’an tsaron CJTF domin yaƙar ‘yan ta’addar Boko Haram a jihar.

Honorabul Audu Bukar Gadaka, ya ce gwamnan ya yi tasiri ga rayukan marasa galihu a cikin Fika da sauran ƙananan hukumomin jihar inda ya buƙace su da su tallafa wa yawancin shirye-shiryensa.

Honorabul Audu Bukar Gadaka ya jinjinawa Gwamna Mai Mala Buni ta fuskar haɓaka ilimi, horas da likitoci, malaman aikin jinya da ungozoma da gina makarantu a cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko da wuraren ba da magani a gundumomi, a cikin ƙananan hukumomi 17, don ingantaccen tsarin kiwon lafiya.

Honorabul Audu Bukar Gadaka ya buƙaci al’ummar ƙaramar hukumar Fika da su shiga cikin shirin noma da shirin gwamna inda gwamnati ta samar da kayan amfanin gona don bunƙasa noma.

Honorabul Audu Bukar Gadaka ya shawarci matasa da su kasance jakadan yankin a kodayaushe.

Ya buƙaci matasa da su yi biyayya ga dokokin tsarin mulki da dokokin ƙasa, su guji shan miyagun ƙwayoyi, su riƙa saurare da mutunta dattijai a cikin al’ummarsu ko yankin da ke sana’ar kasuwanci da koyar da sana’o’i domin dogaro da kai.

Honorabul Audu Bukar Gadaka, ya shawarci dattawan yankin da su tallafa wa shirye-shiryen gwamnati wajen gina ƙaramar hukumar.

Honorabul Audu Bukar Gadaka , ya ce salon jagoranci na gwamna Honorabul Mai Mala Buni na tare da kafa harsashin da ministan harkokin ‘yan sanda na yanzu Sanata Ibrahim Gaidam ya kafa.

Honorabul Audu Bukar Gadaka ya shawarci takwarorinsa shugaban ƙananan hukumomi 17 da su fara gudanar da shirye-shiryen Gwamna Mai Mala Buni da su kasance masu riƙon amana ga jama’arsu, domin suna sa ran za a kai musu ribar dimokuraɗiyya.

Honorabul Audu Bukar Gadaka ya shawarci ma’aikatan ƙaramar hukumar Fika da su sadaukar da kansu wajen aiki tuƙuru, kan lokaci, kuma su guji ɓata lokaci wajen aiki, ya kuma buƙaci ma’aikatan lafiya da su guji ɓata lokaci a bakin aiki.

Honorabul Audu Bukar Gadaka ya shawarci matasa, dattijai a cikin al’umma, Fika musamman da su yi wa ƙasa addu’a, ya kuma jajanta wa al’ummar jihar Borno, gwamnan zartarwa Farfesa Baba gana Zulum da Shehun Borno kan bala’in ambaliyar ruwa ya buƙaci a yi musu addu’a. attajirai da ke ba da agaji don ba da gudummawa ga wadanda ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a ƙarshen shekarar da ta gabata.

 Honorabul Audu Bukar Gadaka ya yaba wa gwamnan bisa samar da sufurin zamani zuwa layin Yobe domin tallafawa rage raɗaɗin talauci.

Honorabul Audu Bukar Gadaka ya yaba da salon jagorancin Sarkin Fika da Sarkin Gudi, da shugabancin babbar jam’iyyar APC ta ƙasa ƙarƙashin Dr Abdullahi Ganduja APC da shugaban jam’iyyar na jihar Yobe Honorabul Muhammad Gadaka.

Honorabul Audu Bukar Gadaka ya jajantawa gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar Borno, Shehun Borno, Shehu Garbai El-kanami da ƙaramar hukumar Jere kan iftila’in da ya shafi jihar a shekarar da ta gabata, ya yi kira ga masu hannu da shuni da su ci gaba da tallafawa waɗanda abin ya shafa.