Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Shugaban Ƙaramar Hukumar Mulki ta Koko/Besse da ke Jihar Kebbi Honarabul Yahaya Bello Koko ya bai wa ofishin hukumar ‘yan sanda motoci biyu ƙirar Peogeot 406 tare da gyara Hilux da ta lalace a ƙaramar hukumar.
Honarabul Bello ya bayyana cewa ya lura da yadda jami’an ‘yan sandan ke wahala bisa ga rashin abin hawa sanadiyyar lalacewar motar da su ke amfani da ita ƙirar Hilux da su ke sintiri da aikin ofis da ita duk da irin matsalar tsaro da ke barazana a wannan yankin.
Ya ce ya zama wajibi a haɗa hannu da jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da ke aiki don bai wa al’umma da dukiyoyinsu kariya.
Ya nemi al’umma da su bai wa jami’an tsaro da sarakuna goyon baya wanjen wanzar da tsaro faɗin yankin ta hanyar kai rahoton duk wani abu ko gungun mutane da ba su yarda da shi ba don ɗaukar matakin da ya dace a asirce.
Ya kuma bayar da tabbacin kawowa kowane ɓangaren tsaro da ke aiki a yankin ƙaramar hukumar ɗauki a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso, su kuma jami’an tsaro ya nemi su bai wa jama’arsa haɗin kai wajen kai agaji a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.