Daga GAMBO ISA
Shugaban ƙaramar Hukumar Nafada, a Jihar Gombe, Honorabul Babangida Adamu Jigawa ya yaba wa gwamnan jihar, Maigirma Muhammad Inuwa Yahaya kan cigaban jihar da yake samarwa a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ciki har da jaridar Blueprint a Abuja.
Ya zayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnan ya samu a ɓangaren cigaban ɗan adam, samar da ababen more rayuwa da raya ƙasa, noma da kiwo.
Ilimi, cibiyoyin kiwon lafiya, gina manyan tituna a karamar hukumar da sauransu.
Honorabul Babangida Adamu Jigawa, ya cigaba da bayyana wasu nasarorin da suka haɗa da, wayar da kan mutane, shirye-shirye kamar gina kasuwar zamani a ƙaramar hukumar Nafada.
Honorabul Babangida Adamu Jigawa ya yabawa aikin gina titunan garin Nafada da sauran ƙananan hukumomin jihar, inda ya ce kuma a fannin yaƙi da masu tada ƙayar baya da rashin tsaro, gwamnatinsa ta bai wa jami’an tsaro ƙwarin gwuiwa ta hanyar duba yanayin tsaro tare da yin kira ga al’ummarsa da su kasance masu ƙaunar zaman lafiya a kodayaushe.
Honorabul Babangida Adamu Jigawa ya ce gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya yi tasiri ga rayuwar marasa galihu da gajiyayyu a ƙaramar hukumar Nafada da sauran ƙananan hukumomin jihar, inda ya buƙace su da su tallafa wa da yawa daga cikin shirye-shiryensa.
Honorabul Babangida Adamu Jigawa ya buƙaci al’ummar ƙaramar hukumar Nafada da su shiga cikin shirye-shiryen shirin noma da kiwo na gwamna inda gwamnati ta samar da kayan amfanin gona don yin noma da kiwo kyauta.
Honorabul Babangida Adamu Jigawa, ya shawarci matasa da su kasance jakadun yankin nagari a kodayaushe, inda ya buƙace su da su bi dokokin tsarin mulki da dokokin ƙasa, su guji shan miyagun ƙwayoyi, su riƙa saurara da mutunta dattijai a cikin al’ummarsu ko yankinsu, kana su rungumi sana’o’in hannu don dogaro da kawunansu.