Daga UMAR GARBA a Katsina
Shugaban ƙaramar hukumar Safana dake Jihar Katsina, Abdullahi Sani Safana, ya bayyana cewa gwamnatinsa na shirye-shiryen aurar da mata zawarawa da marayu waɗanda suka rasa mazajensu a hare haren ‘yan bindinga a yankin.
Shugaban ya bayyana haka ne ga manema labarai a garin Safana a wata ziyarar da ya kai yankin, domin tantance tasirin aikin samar da tsaro na musamman a ƙaramar hukumar dake kan gaba wajen fuskantar hare haren ‘yan bindinga kamar yadda shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarni.
Safana ya ce, sauke irin wannan nauyi na aurar da waɗanda matsalar tsaro ta rutsa da su musamman mata da ƙananan yara abu ne da gwamnatinsa ta saba yi, a cewarsa gwamnatin ƙaramar hukumar Safana a ƙarqashin jagorancin shi na samar da kayan masarufi ga al’umar yankin don rage masu raɗaɗi.
Shugaban ya ce sannu a hankali zaman lafiya na ƙara dawowa a yankin da ke kan iyaka da Dajin-Rugu, ɗaya daga cikin dazukan da ‘yan bindinga suka kafa dabarsu don addabar jihohin Katsina da Zamfara da kuma Kaduna.
“Kafin wannan lokaci, a kullum ‘yan bindigar sun san inda za su kai hari, amma yanzu za a iya ɗaukar mako guda ba tare da samun rahoton hari ba.” In ji shi.
Ya ƙara da cewa, baya ga ayyukan haɗin gwiwa guiwa da sojoji ke jagoranta, gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya ɗauki matasa da ake kira Community Watch Corps waɗanda aka horar da su tare da basu kayan aikin da suka dace don kare al’ummar jihar.
“Akwai motocin sulke da ke sintiri a koda yaushe tare da ‘yan banga na gida da kuma Civilian JTF daga Borno, shi ya sa a yanzu muke samun kwanciyar hankali.” in ji shi.
A cewar shugaban ƙaramar hukumar ta Safana, saboda ‘yan bindinga sun toshe hanyoyin kasuwanci ana iya ganin yawaitar talauci a tsakanin al’ummarsa, wanda hakan ya sa suke taimaka musu a duk lokacin da suke da buƙata.
“Kamar yadda nake magana da ku yanzu, baya ga taimakon da muke baiwa jama’a don biyan buƙatunsu na yau da kullun, muna kuma ɗaukar nauyin bikin auren ’yan mata da matan da suka rasa mazajensu sakamakon hare haren.
“Ya zuwa yanzu mun ɗaura aure har guda 13 kuma ana shirin ƙara haɗa wasu aurarrakin, dole ne mu yi hakan domin mu dakile baɗala”. In ji shugaban ƙaramar hukumar.