Daga JAMEEL GULMA a Kebbi
Sugaban ƙaramar Hukumar mulki ta Yawuri, Honorabul Abubakar Shu’aibu (ƙauran Yawuri) ya yi kira ga al’umma da su guji sayen kaya daga hannun wadanda ba su sani ba musamman masu sana’ar sayen tsofaffin kayayyaki.
Ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ke ganawa da wakilinmu a garin na Yawuri farkon makon nan.
Honarabul Shu’aibu ya bayyana cewa a duk lokacin da wani mutum ya kawo waɗansu kaya musamman kayan da aka yi amfani da su da aka fi sani da turis ko kuma taba-jiki to su tabbatarda sahihancin kayan kafin su saye. Sai da yawa mutane masu gaskiya ke fadawa tarkon wahala kafin a tabbatarda gaskiyar su sun wahala kuma sunansu ya baci.
Bayan wannan kuma yana taimakawa wajen rage sace-sace saboda duk lokacin da barawo ya tabbatar da sai an gudanar da ƙwaƙƙwkwaran bincike kafin a sayi kayansa to ba shakka zai yi wa kan sa ƙiyamul-laili ko kuma ya ƙara gaba, haka kuma sabon shiga zai daina.
A duk lokacin da ɓarawo ya nemi a sayi kayansa bai sami mai saye ba to ko dai ya daina ko kuma ya kara gaba saboda haka mu ke kira ga al’umma musamman masu tu’ammali kayan da aka yi amfanin da su da kuma Yan gwangwan.
Ya ƙara da cewa yanzu haka gwamnati ta ɗauki kwakwkwaran matakin daƙilewa tare da ladabtarwa ga duk wanda aka sami da hannu dumu-dumu cikin harkokin sace-sace komai mukaminsa ta hanyar hadingwiwa tsakanin karamar hukumar mulki ta Yauri da dukkanin jami’an tsaro da ke aiki a ƙaramar hukumar mulkin.
ƙauran na Yawuri ya bayyana cewa idan al’umma suka ƙauracewa sayen kayan sata musamman ga mutanen da basu sani ba lallai wannan zai taimaka matuƙa wajen magance matsalolin sace-sacen ababen hawa da kayan ƙarafa da sauran kayan jama’a.
Su san asalin da sana’ar wanda zasu saye kayan a wurinsa, Su baiwa jami’an tsaro rahoton dukkanin wanda ba su yarda da shi ba, su yi kasuwanci kaɗai da waɗanda akasan ainihin sana’arsu.