Shugaban Ƙasar Ghana ya buƙaci Buhari ya daina roƙon ƙasashen yammaci rance

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Ƙasar Ghana, Mista Nana Akufo-Addo, ya buƙaci Shugaban Nijeriya, Muhammad Buhari, da sauran takwarorinsa na Afirka da su daina roƙon lamunin rance daga ƙasashen yammacin duniya, domin nahiyar Afrika ta samu karɓuwa a duniya.

Shugaban na Ghana ya bayyana haka ne yayin jawabin buɗe taron shugabannin ƙasashen Amurka da Afirka da ke gudana a birnin Washington a ranar Talata 13 ga watan Disamba, 2022.

A cewarsa, ƙasashen Afirka za su haskaka cikin ƙasashen da suka cigaba idan har nahiyar ta daina bara.

Ya ba da shawarar cewa, a yi amfani da albarkatun da ke nahiyar Afirka a nahiyar domin samun cigaba da samun karɓuwa.

“Idan muka daina zama mabarata, muka kashe kuɗaɗen Afirka a cikin nahiyar, za a girmama kowa Afirka, za mu sami girmamawar da ta dace da mu. Idan muka samu wadata kamar yadda ya kamata, girmamawa za ta biyo baya,” inji Akufo-Addo.

Shawarar Akufo-Addo ta zo ne a ranar da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya amince ya bai wa Ghana rancen dala biliyan 3 (£2.4bn) don rage koma bayan tattalin arzikin da ba a tava gani ba a ƙasarsa.

Tuni dai Ghana daman ta fara fama da ɗimbin basussuka, tana fuskantar hauhawar farashi fiye da kashi 40% da faɗuwar darajar kuɗinta, inda matsalolin tattalin arziki sun ƙara ta’azzara tun lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine.

Kusan shugabanni da wakilai 50 na Afirka sun hallara a birnin Washington DC domin wani muhimmin taro da shugaba Joe Biden ya shirya.