Shugaban Ƙasar Sin ya jaddada aniyar Sin da dogaro da kanta ta fannin kimiyya da fasaha

Daga CMG HAUSA

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya jaddada aniyar ƙasarsa na ci gaba da tallafa wa fannin kimiyya da fasaha bisa ikon da ƙasar ke da shi a kashin kanta, tare da bayyana aniyar ƙasar Sin na ƙara bunkasa cigaban ƙasa ta hanyar dogaro da kanta, da tsayawa da kafafunta, da kuma kiyaye tsaron ci gaban ƙasar.

Xi ya yi wannan tsokaci ne a jiya Talata a lokacin da ya kai ziyarar aiki zuwa Wuhan, babban birnin lardin Hubei da ke tsakiyar ƙasar Sin.

Fassarawar Ahmad Fagam

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *