Shugaban ƙasar Sin ya yi shawarwari da takwaransa na ƙasar Cuba

Daga CMG HAUSA

Da safiyar yau Jumma’a 25 ga wata ne shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya yi shawarwari da takwaransa na ƙasar Cuba Miguel Diaz-Canel, wanda shi ne sakatare na farko na kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Cuba, wanda kuma a yanzu haka yake ziyarar aiki a nan birnin Beijing, hedkwatar ƙasar Sin.

A yayin shawarwarin, Xi ya ce, ƙasar Cuba, ita ce ƙasa ta farko da ta ƙulla hulɗar diplomasiyya a tsakaninta da jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin a bangaren yammacin duniya.

Kuma hulɗar da ke tsakanin Sin da Cuba, ta zama abun misali a fannin haɗin gwiwar da ke tsakanin ƙasashen gurguzu, da kuma taimakawa juna a tsakanin ƙasashe masu tasowa cikin sahihanci.

Ya ce ƙasar Sin na son ƙara zurfafa amincewar juna ta fuskar siyasa a tsakaninta da Cuba, da haɓaka haɗin gwiwar a-zo-a-gani a tsakanin ƙasashen 2, da mara wa juna baya kan batutuwan da suke shafar babbar moriyar juna, da taimakawa juna a al’amuran ƙasa da ƙasa da na shiyya-shiyya, da raya ƙasa ta gurguzu mai halin musamman kafaɗa da kafaɗa, da kuma zurfafa hulɗar da ke yi tsakanin Sin da Cuba a sabon zamani.

A nasa ɓangaren, Miguel Diaz-Canel ya ce, ziyararsa ta nuna yadda Cuba ke ɗora muhimmanci kan raya hulɗar haɗin gwiwa a tsakaninta da Sin.

Kazalika Cuba ta amince da yadda kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta ƙasar Sin karkashin shugabancin Xi Jinping, babban sakataren jam’iyyar, ya ba da gudummowa a tunani da aiki, a fannin raya ƙasar gurguzu mai halin musamman na ƙasar Sin a sabon zamani, lamarin da a ganin Cuba, ya ƙarfafa gwiwar dukkan sassan duniya masu ƙoƙarin samun ci gaba sosai.

Mai fassara: Tasallah Yuan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *